Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

- Ministan Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya su daina dogara kan gwamnati

- Adadin matasan dake neman aiki yanzu ya ninka adadin aikin da gwamnatin ke da shi, Aregbe ya bayyana

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya shawarci matasan Najeriya su nemi tayi domin samawa kansu aikin yi saboda gwamnati ba zata iya bai kowa aiki ba.

Ya yi gargadin cewa dogara kan gwamnati ba zai magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya ba.

Aregbesola ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan samawa mata da matasa aiki a yankin Osun ta tsakiya a jihar Osun.

A makonni biyu da suka gabata, ministan ya yi ganawa da kungiyoyi daban-daban a fadin jihar bisa ga umurnin shugaba Muhammadu Buhari bayan zanga-zangar #EndSARS da akayi a watan Oktoba.

Diraktan yada labaran ma'aikatar shiga da fice, Mohammed Manga, ya nakalto Aregbesola da cewa ayyukan gwamnati sun yi kadan idan aka hada da adadin daliban da ke kammala karatu kowace shekara.

Saboda haka, ya ce wajibi ne su nemawa kansu mafita domin samun kudi.

Ya ce ma'aikatar ta fara daukan mutane 5000 aikin hukumar NSCDC. Ya jaddada cewa mutane kadan kawai zasu samu shiga daga kowace karamar hukuma a fadin tarayya saboda yawan adadin marasa aikin yi.

KU DUBA: Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya

Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari
Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: An yi garkuwa da dogarin Minista Pantami, ya samu kubuta

A wani labarin kuwa, biyo bayan tsoron barkewar annobar korona a karo na biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin ganawa da mambobin kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Legit.ng ta ruwaito cewa fadar Shugaban kasa ce taa sanar da hakan a shafinta na Twitter a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

An tattaro cewa taron, wanda zai gudana a fadar Villa da ke Abuja baya rasa nasaba da hauhawan wadanda suka kamu da cutar a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng