Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya

Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bayyana jihohi uku da suka debi kaso mafi yawa wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya

- Acewar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da COVID-19, jihohin sune Legas, Abuja da Kaduna

- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana dalilin da ya sa hakan ya faru

Yayinda ake tsoron sake kakaba dokar kulle karo na biyu a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana Legas, Kaduna da Abuja matsayin manyan cibiyoyin kamuwa da Korona.

Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan ranar Litnin, 21 ga Disamba, a Abuja yayin hira da manema labarai, ThisDay ta ruwaito.

A cewar shugaban kwamitin PTF, wadannan jihohin ne suka kwashi kashi 70% na adadin masu Korona a Najeriya.

Kawo ranar Litinin, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta tabattar da cewa adadin wadanda cutar Korona ta kama a Najeriya na gab da 80,000.

Boss Mustapha ya ce ummul haba'isin hauhawar adadin masu kamuwa da cutar Korona ba komai bane illa taruwan jama'a, da kuma watsi da dokokin kare kai da hukuma ta gindaya.

KU DUBA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya
Jihohi 3 da suka jefa Najeriya cikin halin Korona: Sakataren Gwamnatin Tarayya Hoto: @NCDCgov
Source: UGC

KU KARANTA: Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita

A bangare guda, Boss Mustpha, sakataren gwamnatin tarayya ya ce 'ya'yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, jaridar The Cable ta wallafa.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya.

Sakataren gwamnatin tarayyan ya killace kansa a makon da ya gabata sakamakon mu'amala da yayi da masu cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel