Da duminsa: An yi garkuwa da dogarin Minista Pantami, ya samu kubuta
- An kashe mutane 349 a Najeriya a watan Nuwamban da ya gabata
- Hakzalika an yi garkuwa da mutane 290 a cikin jihohi 23 a fadin tarayya
- Garkuwa da mutane da kisan kai sun zama ruwan dare a Najeriya
Wani jami'in dan sanda kuma dogarin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane amma ya samu kubuta.
Dan sandan, wanda dan asalin jihar Nasarawa ne, yana kan hanyar zuwa Abuja daga Doma a karshen makon da ya gabata akayi garkuwa da shi a Ikari, wani kauye dake Gudi karkashin karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.
Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na dare yayinda yan bindigan suka tare hanya, suka yi fashi, sannan sukayi awon gaba da mutane hudu.
Ya ce an tura yan sanda wajen, kuma yayinda suke bincike, sai gashi ya fito daga cikin daji da jini a gaban goshinsa.
Mai idon shaidan ya bayyana cewa mutumin ya bayyanawa yan sanda cewa ya samu nasarar doke daya daga cikin yan bindigan ne kafin ya gudu daga mabuyarsu.
Ya ce yayinda ya fara gudu, daya daga cikin yan bindiga ya jefe shi da adda kuma ya ji masa rauni a gaban goshi, amma bai daina gudu ba har sai da ya tabbatar ya tsira.
Wata majiya a ma'aikatar ta tabbatar da aukuwan lamarin ga Daily Trust.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce suna bincike kan lamarin.
KU DUBA: Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita
KARANTA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari
A bangare guda, gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su daina cire N20 yayinda mutane ke kokarin duba lambar katin zama dan kasa da akafi sani da NIN.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya bada umurnin a jawabin da ya saki ranar Juma'a.
Sakamakon wannan umurni, yan Najeriya zasu iya samun lambar NIN kyauta idan suka danna *346# a wayansu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng