A watan Nuwamba kadai, an sace mutane 290, an kashe 349: Kalli jerin jiha-jiha

A watan Nuwamba kadai, an sace mutane 290, an kashe 349: Kalli jerin jiha-jiha

- Bayan rayukan da akayi rashi a watan Oktoba sakamakon zanga-zangar EndSARS, an sake rashin rayuka a Nuwamba

- Daga kashe-kashen da yan Boko Haram ke yi, sannan hare-haren yan bindiga

- Hakazalika rikici matasa masu tada zaune tsaye a fadin tarayya sun kashe junansu

Akalla mutane 349 aka hallaka a watan Nuwamba a hare-hare a fadin Najeriya, rahoton wata kungiya mai zaman kanta, Nigeria Mourns, ya nuna.

Rahoton mai taken "Rahoton hare-hare: Nuwamba 2020," ya bibiyi kashe-kashen da akayi a fadin tarayya.

Kungiyar na amfani da rahotannin jaridu da bayanin iyalai domin tattara bayananta.

A cewar rahoton, an kai hare-hare jihohi 23 a watan Nuwamba.

Lissafin ya nuna cewa cikin mutane 349 da aka kashe, 309 masu farin hula ne yayinda 40 jami'an tsaro.

Hakazalika, an yi garkuwa da mutane 290 a watan Nuwamba.

Jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya, wacce ke fuskantar ta;'addin Boko Haram, ce ta debi kaso mafi yawa na wadanda aka kashe.

Bayan jihar Borno, yadda aka samu kashe-kashe a jihohin Najeriya ya nuna cewa matsalar tsaro bai kebanta ga wanin sashen Najeriya ba.

Misalin jihar Edo ta biyo jihar Borno na adadin mutanen da aka hallaka a Nuwamba.

KU KARANTA: Kada ku dogara da gwamnati don samun aiki, Ministan Buhari

A watan Nuwamba kadai, an sace mutane 290, an kashe 349: Kalli jerin jiha-jiha
A watan Nuwamba kadai, an sace mutane 290, an kashe 349: Kalli jerin jiha-jiha
Asali: Original

KU DUBA: Matashi dan Najeriyan da ya auri baturiya sa'ar mahaifiyarsa ya rabu da ita

Ga jerin jihohin da adadin wadanda suka rasa:

Borno – 162, Edo – 57, Kaduna – 55, Katsina -12, Delta – 11, Zamfara – 10, Oyo – 5, Ondo – 5, Enugu – 4, Kogi -3, Kano – 3, Ekiti – 3, Adamawa – 3, Bayelsa – 3, Cross River – 2, Nasarawa – 2, Niger – 2, Rivers – 2, FCT – 1, Akwa Ibom – 1, Ebonyi – 1, Ogun – 1 and Sokoto – 1.

Game da wadanda sukayi wannan kashe-kashe, rahoton ya nuna cewa yan ta'addan Boko Haram suka kashe 149; yan bindiga sun hallaka 86; yayinda rikicin yan daba yayi sanadiyar rayukan 62.

A wani labarin, gwaman jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna ɓacin ransa kan wani sabon hari da kungiyar yan ta'adda ta Boko Haram ta kai akan wasu matafiya a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Gwamnan wanda ya ziyarci Jakana, ɗaya daga cikin manyan garuruwan dake kan babbar hanyar Maiduguri-Damaturu, ya nuna matuƙar fushinsa kan sojojin bisa sace matafiyan da yan Boko Haram suka yi.

A cikin jawabin da ya fitar domin bayyana fushinsa, Zulum ya tambayi rundunar soji cewa ta ''yaya kuke sa ran zamu gamsu akan cewa zaku iya karemu, ku kawo karshen Boko Haram, idan har ba zaku iya tabbatar da tsaro a kan hanya mai nisan kilomita 20 ba?".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel