Tsaro: Sokoto, Adamawa da Benue sun bada umurnin kulle makarantu da gaggawa

Tsaro: Sokoto, Adamawa da Benue sun bada umurnin kulle makarantu da gaggawa

A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai a makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Haka ya jefa rudani cikin sauran jihohin dake da iyaka da jihar Katsina saboda gudun kada irin haka ya fada musu.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bada umurnin kulle makarantun kwana 16 dake iyaka da makwabtanta.

A jawabin da aka saki ranar Alhamis, gwamnatin ta yanke shawaran ne a taron majalisar tsaron bisa shawarar kwamishanan ilmin makarantun firamare da sakandare, Dr Muhammad Bello Guiwa.

Ga jerin makarantun da aka kulle:

GGMSS Illela, Sultan Muhammadu Tambari Arabic Secondary School, Illela, Gamji Girls College, Rabah, Government Secondary School, Gada, Government Secondary School, Gandi da Government Secondary School, Goronyo.

Hakazalika akwai Government Secondary School, Isa, Government Secondary School Sabon Birnin Gobir, Boarding Primary School, Isa, Boarding Primary School, Balle da makarantar kwana ta firamare, Jabo.

Sauran sune UBE Junior Secondary School, Sabon Birni, Government Secondary School, Kebbe, Government Secondary School, Tureta, Government Technical College, Binji da Olusegun Obasanjo Technical College, Bafarawa.

Gwamna Tambuwal ya ce "za'a kulle makarantun ne na tsawon makonni biyu tukun."

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako

Tsaro: Sokoto, Adamawa da Benue sun bada umurnin kulle makaratu da gaggawa
Tsaro: Sokoto, Adamawa da Benue sun bada umurnin kulle makaratu da gaggawa
Source: Getty Images

DUBA NAN: Daliban Kankara: Ina neman afuwa, ku yafe min: Garba Shehu ga yan Najeriya

A jihar Adamawa kuwa gwamna Ahmadu Fintiri, ya bada umurnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ranar Juma'a, 18 ga Disamba, 2020, NAN ya ruwaito.

Hakan na kunshe cikin jawabin da sakataren yada labaran gwamna, Mr Humwashi Wonosikou, ya saki ranar Juma'a a Yola.

Hakazalika a jihar Benue gwamna Samuel Ortom, ya bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana a jihar lokacin da ya ziyarci cibiyar tsaro ta MSCC a Makurdi, birnin jihar.

NAN ta nakalto jawabinsa da cewa ya kulle makarantun ne matsayin rigakafi daga garkuwa da dalibai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel