Daliban Kankara: Ina neman afuwa, ku yafe min: Garba Shehu ga yan Najeriya
- Bakin nasarar kubutar daliban GSSS Kankara, Malam Garba Shehu ya janye maganarsa
- Bayan garkuwa da yaran, kakakin Buharin ya ce dalibai 10 kadai aka sace
- Yan Najeriya sun bude masa wuta kuma sunce wajibi ne sai ya janye maganarsa
Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya nemi afuwan yan Najeriya kan maganar da yayi cewa dalibai 10 kacal aka sace a makarantar Kankara.
Ya bayyana cewa ba da gangan yayi ba ko dan shashantar da sace yaran ba, amma bayanin da ya samu ne ba gaskiya ba.
Yace: "Ina mai neman afuwa dangane da kuskuren da na yi, inda na ce adadin daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kankara (GSSS) da aka yi garkuwa da su, su 10 ne.
Ba da gangan na yi wannan furucin ba. Na samu wannan bayani da na sanar a lokacin, daga bakin wadanda ya kamata a ce sun san hakikanin adadin kafin su sanar da ni cewa su 10 ne.
Dalili kenan aka ga adadin yawan da na furta, ko kusa bai kai yawan wadanda ake cigiya ba a lokacin.
Tare da neman afuwa, ina so a fahimci ban isar da wancan sako ba domin rage yawan su da gangan.
Ina rokon a karbi uziri na kan wannan lamari. Mu ci gaba da kokarin da mu ke a kai na ganin mun maida Najeriya Kasaitacciyar Kasa."
KU KARANTA: Kai tsaye: Buhari na ganawa da daliban Kankara 344 (Hotuna)
KU KARANTA: GSSS Makaranta: Lai Mohammed yace Najeriya ta samu agajin kasashen waje
Mun kawo muku cewa a ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 344.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan.
A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng