Ya kamata ka farga haka ko mu dauki mataki mai tsauri a kan ka; Sanatoci sun kwankwashi Buhari

Ya kamata ka farga haka ko mu dauki mataki mai tsauri a kan ka; Sanatoci sun kwankwashi Buhari

- Mambobin majalisar dattijai sun gaji da alkunyar da suke yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari

- Wasu daga cikin mambobin majalisar sun bayyana cewar shugaba Buhari ba zai taba sauyawa ba

- A cewar wasu mambobin, ya kamata shugaba Buhari ya sani cewa doka fa ta basu ikon tsige shugaban kasa

Sanatoci a ranar Talata sun koka akan gazawar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wajen shawo matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fama da ita, kmar yadda Punch ta rawaito.

Sun kuma tunawa Shugaban ƙasar irin ƙarfin ikon da doka ta basu na tsige Shugaban ƙasa kamar yadda yake a kundin dokokin Najeriya.

Sanatoci sun yi niyyar ɗaukar ƙwararan matakai da suka haɗar da dakatar da kasafin kuɗin 2021, wanda hakan zai tilastawa shugaban ƙasa aiwatar da ƙudirinsu da gaske.

Sanatocin sun yi magana ne lokacin muhawara kan wani ƙudiri da Sanata Bello Mandiy, mai wakiltar Katsina ta kudu, ya gabatar akan sace yara 350 na makarantar Sakandire, wanda Boko Haram ta ɗauki nauyin aikata hakan.

KARANTA: An dakatar da shugaban kwalejin kimiyya bayan an gano katafaren gado girke a ofishinsa

Sanatoci sun ƙara da cewa ba su ga amfanin shugabannin tsaro na yanzu ba, suna buƙatar canji.

Ya kamata ka farga haka ko mu dauki mataki mai tsauri a kan ka; Sanatoci sun kwankwashi Buhari
Ya kamata ka farga haka ko mu dauki mataki mai tsauri a kan ka; Sanatoci sun kwankwashi Buhari @Bashirahmad
Asali: Twitter

Kazalika sun bada shawarar a yi amfani da ministan tsaro, janar janar ɗin soja, da kuma shugabannin hukumomin tsaro don kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasa.

Sun kuma yi "tirr da Allah wadai" bisa kai hari makarantar Kimiyya ta Sakandire, Kankara, jihar Katsina, wanda hakan ya haddasa ɓatan wasu ɗaliba masu yawa.

KARANTA: Ganduje ya bayar da umarnin rufe makarantun Kano, ya umarci iyaye su debo 'ya'yansu

Sanatoci sun ƙara shawartar shugaban ƙasa da ya sake duba tare da aiwatar da shawarwari da gyare-gyaren rahoton da kwamitin Sanatoci kan ƙalubalen harkokin tsaron Najeriya ta gabatar masa.

Shugaban kwamitin Sanatoci kan Baitulmali, Mathew Urhoghide, ya ce majalisa ta ƙarar da dukkan abin da ta ke da shi don saka shugaban ƙasa ya daƙile matsalar rashin tsaro.

Urhoghide yace, "mun tsaya tsayin daka kan a sauya shugabannin tsaro. Iyakacin maganar ka, iyakar baƙinciki da haushin da zaka sha kan shugaban ƙasa, ba zai ta ɓa canjawa ba.

Shi ma a nasa ɓangaren, Sanata Sani Musa ya ce, "akwai buƙatar jawo hankalin shugaban ƙasa don ya san cewa ya isa haka, a sallami shugabannin tsaro.

"Ina fatan majalisa zata ɗauki mataki mai tsauri akan haka. Muna da ikon yin hakan.

Sanata James Manager yace, "kamata su san cewa mun yi iyakar ƙoƙarin don ayi abinda ya dace.ya

"Mun saki akalar komai ga Shugaban ƙasa don aiwatarwa, mu dai mun zartar, amma har yanzu ba su aiwatar da ko ɗaya daga ciki ba. Ana magana akan mu gayyato shugabannin tsaro, mu ce musu me, akan wanne dalili?

Sanata Gabriel Suswam ya ce, "Babu abin da yafi muhimmanci ga gwamnati fiye da kare rayuka da dukiyar al-ummarta, a ko ina, kuma koda yaushe."

Shugaban Sanatoci, Ahmad Lawan ya shawarci abokanansa sanatoci kan kada su gajiya ko su saduda da yin magana.

Ya ce, "A matsayin mu na masu zartar da doka, kada mu taɓa gajiya da magana akan batuwan da suka shafi al-ummarmu."

A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin fara zaman dirshan akan sace dalibai akalla 333 a sakandiren Kankara, jihar Katsina.

Fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana suka yi awon gaba da su.

'Yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng