Ganduje ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Jihar Kano

Ganduje ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Jihar Kano

- Jihar Kano ta bi sahun Kaduna da Jigawa wajen bayar da umarnin rufe dukkan makarantunsu

- A yayin da wasu jihohin arewa ke rufe makarantun saboda dawowar annobar korona, wasu kuma don tsaro ne

- Gwamnatin Jihar Kano ba ta bayyana dalilin bayar da umarnin rufe makarantun

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin Jihar.

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba a cikin gajeriyar sanarwar da kwamishinan ilimi, Sanusi Kiru, ya fitar, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

"Mai girma gwamna ya bayar da umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili

"Ana umartar iyayen da ke da yara a makarantun kwana su je domin dauko 'ya'yansu zuwa gida daga gobe, Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020.

Ganduje ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Jihar Kano
Ganduje ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Jihar Kano @Dawisu
Asali: Twitter

"Gwamnati ta na bayar da hakuri a bisa dukkan wani rashin jin dadi da daukan wannan mataki ya haifar," kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa sanarwar da kwamishinan ya fitar.

DUBA WANNAN: An dakatar da shugaban kwalejin kimiyya bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa

Legit.ng ta wallafa labarin cewa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana manyan dalilan da suka sa shi ya tuɓe Muhammadu Sunusi II daga karagar sarkin Kano, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Gwamnan ya bayyana tuɓe sarkin a matsayin matakin gaggawa don ceto tsarin mulkin masarautar gargajiya daga kama-karya.

Gwamna Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin ƙaddamar da wani littafi da aka rubuta akan rayuwar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda shahararren dan jaridar nan, Bonaventure Philips Melah, ya rubuta kuma ya wallafa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: