An dakatar da shugaban kwalejin kimiyya bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta Ede ta sanar da dakatar da shugabanta, Adekunle Masopa
- Sanarwar dakatar da Masop ta fito ne bayan ziyarar da kwamitin ma'aikatan makarantar ya kai ofishinsa
- Kwamitin ya ziyarci ofishin ne domin ganewa idonsa bayan samun korafin cewa Masop ya na sharbar bacci a ofis
Hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da fasaha (Polytechnic) ta Ede da ke Jihar Osun, ta dakatar da shugaban makarantar, John Adekolawole, bisa zarginsa da kwasar bacci a lokacin aiki, kamar yadda lindaikeji ta wallafa.
Adekunle Masopa, wanda shine shugaban ma'aikata na makarantar (ASUP) ne ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa dogaro da dalilai 21 da suke zargin shugaban makarantar da aikatawa.
Da ya ke magana da manema labarai bayan taron gaggawa da kungiyar ta yi, Masopa ya ce suna zargin Adekolawole da rashin girmama ofishinsa na shugaban makaranta tare da sanya makeken gado na alfarma wanda ke ba shi damar yin bacci lokacin aiki.
KARANTA: Katsina: Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban Kankara, ta fadi dalili
"Mun gaji da kawo kararsa da ake yi, don haka ne ma'aikatan wannan makaranta suka yanke shawarar ɗaukar mataki na karshe." A cewar shugaban ma'aikatan makarantar.
Ya kara da cewa, "Laifukan da suka janyo ɗaukar wannan mataki sun haɗa da: kauracewa gun aiki har na tsawon wata guda da kuma cin zarafin babban ofishinsa ta hanyar saka gado domin yin bacci."
KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"
A baya Legit.ng ta rawaito cewa CNG sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaban kasa, Muhamadu Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.
Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng