Jita-jita ne kawai: Mai magana da yawun Alkalin Alkalai ya karyata rahoton cewa ya kamu da Korona

Jita-jita ne kawai: Mai magana da yawun Alkalin Alkalai ya karyata rahoton cewa ya kamu da Korona

- An samu sabani tsakanin Alkalin kotun da koli da kakakin kotun koli

- Sabanin fahimtan shine kan gaskiyar halin shugaban Alkalan Najeriya CJN, Tanko ke ciki

- Yayinda wani abokin aikin CJN yace ya kamu da Korona, kakakin kotun ya ce sam ba haka bane

Diraktan yada labaran kotun koli, Dr Festus Akande, ya ce rahoton cewa Alkali Alkalan Najeriya, Tanko Mohammed, ya kamu da Korona jita-jita ne kawai, Punch ta ruwaito.

Akande ya bayyana hakan a jawabin da ya saki bayan wani Alkalin kotuna koli, Ibrahim Saulawa, ya bayyana a wani taro a Abuja cewa Alkalin Alkalan ya kamu da Korona kuma an fitar da shi waje.

Tun a ranar Talata, mai magana da yawun Alkalin Alkalan ya karyata rahoton cewa mai gidansa na rashin lafiya.

Ana kyautata zaton ya saki wannan jawabi na biyu ne domin martani da Alkali Ibrahim Saulawa.

Akande yace: "Biyo bayan jawabin farko da na saki, ina sake jaddada cewa babu wani rahoton asibiti dake nuna Alkalin alkalai ya kamu da cutar Coronavirus."

"Masu yada jita-jita su kara bincike kuma su samo takardar gwajin asibiti da aka dogara da shi."

KU KARANTA: Pantami ya bada umurnin rufe layukan marasa lambar katin zama dan kasa

Jita-jita ne kawai: Mai magana da yawun Alkalin Alkalai ya karyata rahoton cewa ya kamu da Korona
Jita-jita ne kawai: Mai magana da yawun Alkalin Alkalai ya karyata rahoton cewa ya kamu da Korona Credit: Presidency
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamna Matawalle ya kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Kaduna

Mun kawo muku dazu cewa babban alkalin kotun kolin Najeriya, Tanko Muhammad ya kamu da cutar korona.

A halin yanzu babban alkalin yana Dubai, daular larabawa inda yake samun kular kwararrun masana kiwon lafiya.

Daya daga cikin alkalan kotun koli, Mai shari'a Ibrahim Saulawa ya bayyana hakan yayin kaddamar da hedkwatar kungiyar lauyoyi musulmai a ranar Talata a garin Abuja.

A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da manyan lauyoyi a kasar nan 72, amma ba a hango babban alkalin a wurin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel