Da duminsa: CJN Tanko ya kamu da korona, baya Najeriya baki daya
- Jastis Ibrahim Tanko Muhammad, babban alkalin kotun kolin Najeriya ya kamu da korona
- Mai shari'a Ibrahim Saulawa na kotun kolin ya sanar da hakan a ranar Talata a garin Abuja
- Babban alkalin a halin yanzu yana Dubai, daular Larabawa, inda yake samun tallafin likitoci
Babban alkalin kotun kolin Najeriya, Tanko Muhammad ya kamu da cutar korona, The Nation ta ruwaito.
A halin yanzu babban alkalin yana Dubai, daular larabawa inda yake samun kular kwararrun masana kiwon lafiya.
Daya daga cikin alkalan kotun koli, Mai shari'a Ibrahim Saulawa ya bayyana hakan yayin kaddamar da hedkwatar kungiyar lauyoyi musulmai a ranar Talata a garin Abuja.
A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da manyan lauyoyi a kasar nan 72, amma ba a hango babban alkalin a wurin ba.
Mataimakinsa ne ya tsaya a madadinsa inda ya bai wa manyan lauyoyin rantsuwa a kotun kolin.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta
KU KARANTA: JNI ta fallasa wadanda basu son a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
Idan za mu tuna, mutane suna ta yada labaran cewa ba shi da lafiya, kansancewar bai bayyana a kotu ba ranar bikin rantsar da manyan lauyoyi 72 na Najeriya. An dade ba a ganin babban alkalin, mai shekaru 66 a bainar jama'a.
Taron da aka yi na rantsar da manyan lauyoyi, wanda aka yi shi a kotun koli ya dauki hankali kwarai. Rashin ganin CJN a kotun ba abu bane wanda aka saba da shi, saboda shine yake gudanar da abubuwa da dama a ranar.
CJN ya rantsar da alkalan kotun koli guda 8 a ranar 6 ga watan Nuwamba, amma tun daga nan ba a ganin shi a cikin mutane.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng