Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya kulle makarantun Zamfara dake makwabtaka da Katsina da Kaduna
- Gwamnatin Zamfara ta rufe makarantu goma a jihar don gudun abinda ya faru a Katsina
- Daga cikin makarantun nan akwai na kwana da kuma na jeka da dawo
- Kwamishanan ilmin jihar ya bayyanawa manema labarai dalilin hakan
Labarin dake shigowa da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Zamfara ta bada umurnin kulle dukkan makarantun jihar dake makwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna.
TVC ta ruwaito cewa gwamnatin ta tabbatarwa iyayen daliban makarantun dake cikin Gusau da ba'a kulle ba cewa kada su damu akwai isasshen tsaro a cikin gari.
DUBA NAN: Hazikan soji sun damke 'yan fashi da masu taimaka musu a Zamfara
Kwamishanan ilmin jihar Zamfara, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa ta baiwa gwamnan shawaran rufe wadannan makarantu gudun kada a faru da jihasr Katsina ya afka musu.
Yace: "A nan jihar Zamfara muna kokarin kiyaye faruwan abinda ya faru a Kankara."
"Saboda haka mun baiwa gwamna shawara ya rufe wasu makarantun kwana dake iyaka da jihar Kaduna da jihar Katsina."
"Ba dukkan makarantun kwana dake Zamfara aka rufe ba."
Ga jerin makarantun da gwamnatin jihar ta rufe:
GASS Zurmi
GSS Birnin Magaji
GSSS Bayumkafi
GSS Ape
GSSS Bokuyum
GSSS Dan Sadau
GDSS Nasarawa Malayi
GDSS Gusami
GDSS Gudun Kore
GDSS Tsafe
KU DUBA: Majalisar dattawa ta aika sammaci ga ministan tsaro da shugabannin tsaro kan satar daliban Kankara
Mun kawo muku cewa kungiyar Boko Haram ta sanar da cewa ita ce keda alhakin sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, kamar yadda HumAngle ta rawaito.
A cewar HumAngle, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce har yanzu basu tuntubi kowa dangane da wasu sharuda na sakin daliban ba.
Jaridar ta ce, Shekau ya sanar da hakan ne a cikin wani sakon sautin murya mai tsawon mintuna 4:28 da ya fitar da duku-dukun safiyar ranar Talata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli bidiyin channels:
Asali: Legit.ng