Mun yarda ka yi karatu sosai, amma kayi hakuri: Jami'ar East Carolina ta baiwa Ganduje hakuri

Mun yarda ka yi karatu sosai, amma kayi hakuri: Jami'ar East Carolina ta baiwa Ganduje hakuri

- Jami'ar ECU ta sake aikewa gwamnan jihar Kano wani sako

- Amma wannan karon ta bashi abinda ya bukata na hakuri kan yaudarar da akayi masa

- Abu guda daya kacal ta sake cewa ba zata iya ba sa ba

Jami'ar East Carolina ta baiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, hakuri kan duk wani irin bacin ran da wasikarta na karyata bashi matsayin Farfesa, ya sababba.

Jami'ar ta ce lallai ta samu sakon gwamnan inda ya nemi a bashi hakuri kan abinda ya faru.

Shugaban jami'ar Grant Hayes, ya bayyana a wasikar da ya sake aikewa Ganduje ranar 8 ga Disamba cewa ya yarda da takardun da Ganduje ya aiko na irin karatun da yayi kuma lallai ya cancanci a bashi matsayin.

Hayes ya ce ba da niyyar cin mutuncin Ganduje ya mayar da martani kan labarin nadashi Farfesa ba.

"Na samu sakon ka na ranan 7 ga Disamba, 2020. Kuma na fahimci irin karatuttukan da kayi kamar yadda ya aiko kuma lallai kana da kwarewa irin na Malaman makarantan, " Grant yace.

"Na yi takaicin duk wani irin cin mutuncin da haka ya janyo maka."

KU DUBA: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar

Mun yarda ka yi karatu sosai, amma kayi hakuri: Jami'ar East Carolina ta baiwa Ganduje hakuri
Mun yarda ka yi karatu sosai, amma kayi hakuri: Jami'ar East Carolina ta baiwa Ganduje hakuri credit: bbc.com/hausa
Source: UGC

KU KARANTA:An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis

Mun kawo muku cewa jami'ar kasar Amurka, East Carolina ECU, ta karyata nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Farfesa mai ziyara.

Jaridar Premium Times ta aike wasika jami'ar ranar Alhamis domin tabbatar da sihhancin labarin nadin Ganduje duk da cewa an kama shi a bidiyo yana karban daloli.

A martanin jami'ar, ta bayyana ainihin abinda aka aikewa Ganduje.

Mukaddashin shugaban jami'ar, Grant Hayes, ne ya rattafa hannu kan wasikar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel