Yanzu-yanzu: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis

Yanzu-yanzu: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis

- Kamar yadda ministan shari'a ya fada, Buhari ya fasa gurfana gaban majalisa

- Abubakar Malami ya ce majalisa ba tada hurumin gayyatan Buhari

- Gwamnonin APC sun shawarci Buhari kada a gurfana gaban yan majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amsa gayyatar da yan majalisar wakilan tarayya suka yi masa domin musu jawabi kan tabarbarewan tsaro a fadin tarayya.

Yayinda aka fara zama a zauren majalisa ranar Alhamis, ba a ga alaman shugaba Buhari ba, Channels TV ta ruwaito.

Wani dan majalisa daga jihar Rivers, Solomon Bon, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa har yanzu shugaban kasan bai gurfana ba. Ya bukaci Kakakin majalisa yayi musu bayani.

Kakaki ya amsa tambayarsa inda yace majalisar zata saurari sako wajen wajen shugaban kasan da kansa.

A ranar 1 ga watan Disamba, mambobin majalisar wakilai sun yi ittafakin aike sakon sammaci ga shugaba Buhari domin ya yiwa yan Najeriya bayanin ainihin abinda ke faruwa kan lamarin tsaron kasar.

Wannan abu ya biyo bayan kisan manoma 43 da yan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar Borno.

Martani kan haka, hadimar shugaba kasa, Lauretta Onochie, ta sanar ranar Litinin, 7 ga Disamba cewa Buhari ya amince zai gurfana gaban yan majalisan.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar

Yanzu-yanzu: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis
Yanzu-yanzu: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis
Source: Facebook

Mun kawo muku jiya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis domin jawabin kan tabarbarewan tsaro a fadin tarayya.

Bayani daga bakin mai tsawatarwa a majalisa, Muhammad Munguno, ya nuna cewa shugaban kasan ya canza ra'ayinsa, TVCNews ta samu rahoto.

Ya ce ana kyautata zaton Buhari ya canza ra'ayinsa ne saboda zargin da ake cewa yan majalisan PDP za su ci mutucinsa.

Yan majalisan PDP sun yi ganawar sirri a daren Talata, yace.

DUBA NAN: Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka

Kun ji cewa bayan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan gurfanar Buhari gaban yan majalisun dokokin tarayya.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel