Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar

- Minista Pantami ya ce tun watan Nuwamba yan Najeriya suka samu rahusan farashin Data

- Tun lokacin hawa mulkinsa yake kokarin ganin an rage farashin kan yan Najeriya

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin 'Data' da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC.

Saboda haka, kudin 'Data' na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba), The Nation ta ruwaito.

'Data' kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin 'data' a fadin tarayya.

KU KARANTA: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar
Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar
Asali: Facebook

"Farashin kudin Data ya sauko daga N1000 da ake sayarwa a Junairu 2020, zuwa N487.18 fari daga watan Nuwamba, 2020," Hadimin Pantami, Femi Adeluyi yace.

"Haka yake kunshe cikin rahoton da hukumar sadarwan Najeriya NCC ta aikewa Minista bisa umurnin da ya bayar."

KU KARANTA: Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka

A baya mun kawo muku cewa a binciken da Surshark Press, wani kamfanin a kasar Amurka ya saki, an samu cewa Najeriya na kasa da kasar Kolombiya da Honduras wajen arhan 'Data'.

"Najeriya ce kasa maras rahusan Data a fadin duniya. Tana kasa da Kolumbiya da Honduras wajen rahusan Data," Jawabin yace.

A salon da kamfanin tayi amfani da shi wajen binciken, an lura da tsarin 'data' mafi arha a kowace kasa.

A kan ingancin yanar gizo kuwa, Najeriya ta zo na 81 cikin kasashe 85.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel