Almundahanar ₦2b: Babu wata tuhuma da zan amsa; Maina ya faɗawa kotu
- Duk da cewa hukumar EFCC ta na yi masa tuhuma 12 a gaban kotu, Abdulrasheed Maina ya ce bai aikata laifin komai ba
- Maina, tsohon shugaban tawagar gyaran fansho, ya tsallake beli, ya sulale zuwa kasar Nijar
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa zarginsa da almundanar kudin da yawansu ya kai biliyan biyu
Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho (PRTT), ya shaidawa babbar kotun tarayya a Abuja cewa babu wata tuhuma da zai amsa akan zarge-zargen da Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ke yi masa.
Maina ne ya faɗawa babban alƙalin kotun, Okon Abang, hakan jim kaɗan bayan EFCC ta rufe shari'ar, ta bakin lauyanta, Farouk Abdullahi, a ranar Laraba.
Ya ce kundinsa da kimarsa zasu kasance ba tare da kowanne irin tabo ba nan ba da jimawa ba domin gaskiya za ta bayyana.
Tsohon shugaban hukumar fanshon, ta bakin lauyansa, Anayo Adibe, ya sanar da hakan jim kaɗan bayan ya gama tantance shaida na tara(PW9), Rouqquaya Ibrahim, wata mai bincike a EFCC.
Alƙali Abang ya ɗage shari'ar zuwa ranar juma'a don bawa mai kare wanda ake tuhuma damar yiwa kotu jawabi baki da baki da kuma bawa lauya mai tuhuma damar mai da martani a shari'a mara batu.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Maina a gaban Alƙali Abang a ranar 25 ga watan Oktoba tare da abokan burminsa da suka hada da wani kamfani mai suna 'Common Input Property and Investment Ltd'.
KARANTA: Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria
Duk da cewar ana tuhumarsa da laifuka 12 da suka shafi almundahanar kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan ₦2b, Maina ya yi iƙirarin cewa bai aikita ko ɗaya cikin laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.
An dawo da Maina ga hukumomin Najeriya bayan kama shi a jamhuriyyar Nijar a ranar Litinin.
Ya tsallake beli wanda ya kai ga kama Sanata mai ci, Ali Ndume, wanda ya tsaya masa a kotun kafin a bayar da shi beli.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.
Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.
A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami'an tsaron Najeriya da Nijar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng