Kamfen 2027: Dalilin da Ya Sa Shugaba Tinubu Ya Zaɓi Kano da Wasu Jihohi 11 a Najeriya
- Kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya zaɓi jihohi 12 da zai je kamfen zaɓen 2027
- Alake ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi watsi da gudanar da harkokin mulki domin ya mayar da hankali kan kamfen ba
- Ya bayyana cewa jihohin da aka zaɓa suna da muhimmanci wajen tantance sakamakon zaɓe a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dele Alake, kakakin kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, ya bayyana dalilin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi jihohi 12 da zai kai ziyara domin kamfen zaɓen 2027.
Alaie ya kare Bola Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar ba zai yi watsi da aikinsa na mulki domin yakin neman zabe ba.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023

Source: Facebook
Dele Alake ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Najeriya (NTA), inda ya kare matakin Tinubu na zuwa kamfe wasu jihohi maimakon zuwa kowace jiha.
Alake ya yi magana kan matakin Tinubu
Ya ce shugaban ƙasar yana sane da muhimmancin daidaita ayyukan kamfen da nauyin da ke kansa na jagorantar Najeriya.
Alake, wanda shi ne ministan harkokin ma'adanai, ya ce:
“Ba ya son na ɗauke hankalinsa. Shi ya sa shugaban ƙasar ya bayyana a fili lokacin ƙaddamar da kwamitin kamfen kwanaki kaɗan da suka gabata cewa a yi masa uzuri, domin ba zai yi watsi da gudanar da mulki ya koma kamfen ba.
“Washegari kuma, na ga kanun labarai a wasu jaridu, musamman waɗanda suka yi nazari cikin adalci, inda suka fahimci maganarsa da cewa shugaban ƙasar ba zai yi watsi da mulki domin kamfen ba.
“Akwai kuma wasu ɓangarorin kafafen yaɗa labarai masu mummunan ra’ayi da suka yi ta ihu suna cewa, ‘Oh, Tinubu ba zai je ko’ina ba. Oh, Tinubu ba zai yi kamfen ba,’ da makamantansu, shugaban ƙasar yana da ayyuka da dama a gabansa.
“Gaskiya, a wasu lokuta ina tausaya masa idan ina tare da shi.”
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yake tausayawa shugaban ƙasar duk da cewa Tinubu ya ce kada a tausaya masa, Alake ya ce nauyin shugabancin ƙasar yana da yawa.
Dalilin Tinubu na zabar jihohi 12
Dangne da dalilin zabar jihohi 12, Alake ya ce:
“Idan aka gudanar da bincike na gaskiya kan waɗannan jihohin, za a gano cewa wuraren da ya zaɓa suna cikin jihohin da ke da tasiri wajen tantance wanda zai lashe zaɓe.
"Don haka, babu wata matsala a wannan mataki, kuma ya kamata a yaba wa shugaban ƙasar saboda hakan.”

Source: Facebook
Sunayen jihohin da Tinubu ya zaɓa
Kun ji cewa kwamitin kamfen APC ya tsara cewa Shugaba Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe a birane 12 da ke shiyyoyin siyasa shida na ƙasar nan.
Kano da Kaduna na cikin jihohin Arewa da Shugaba Tinubu zai halarci taron kamfe domin neman kuri'un Najeriya karo na biyu gabanin zaben 2027.
Asali: Legit.ng
