APC ta kori tsohon mataimakin Oshiomhole, ta rushe shugabancin shiyya da jihohi
- Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa ta kori tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin kudu maso kudu; Ntufam Hilliard Eta
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya tabbarwa da manema labarai hakan yayin tattaunawarsa da su
- APC ta gudanar da taron kwamitin zartarwa (NEC) wanda shugaba Buhar da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, su ka halarta
Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC (NEC), a ranar Talata, ya sanar da korar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar mai kula da shiyyar kudu maso kudu, Ntufam Hilliard Eta.
Kazalika, NEC ta sanar da cewa ta rushe zababbun shugabannin shiyya, jihohi, da tarayya.
Jaridar Punch ta rawaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ne ya tabbatar da korar ita yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron.
An yanke shawarar korar Eta yayin taron NEC wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, suka halarta.
KARANTA: Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC, Kwamred Abba Yaro
Korar Eta ba za ta rasa nasaba da karar da ya shigar da jam'iyyar APC da shugabancin rikon kwarya da aka kafa ba.
Batun karar da Eta ya shigar ta zama karfen kafa ga shugabancin riko da Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, ke jagoranta.
Bayan kotu ta sauke tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, jam'iyyar ta tsinci kanta a cikin rikicin shugabanci da rabuwar kai.
Eta ya sanar da kansa a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC bayan tsige Oshiomhole.
A wancan lokacin, Eta ya kafa hujjar cewa shine ya kamata ya zama shugaban jam'iyyar APC saboda yanki kudu maso kudu ne ya kamata ya rike shugabancin jam'iyya idan za'a yi wa kundin tsarin mulkin jam'iyya biyayya.
Sai dai, bayan APC ta kammala taron NEC na lokacin ta sanar da kafa kwamitin rikon kwarya a karkashin Mai Mala Buni, lamarin da bai yi wa Eta dadi ba har ya sa shi garzayawa kotu neman ta bayyana shugabancin Buni a haramtacce.
Legit.ng ta rawaito cewa ma'aikatan wucin gadi guda biyu da suka bace yayin zaben maye gurbi na ranar Asabar a jihar Zamfara sun bayyana.
An samu matsalar satar akwatin zabe da barkewar rikici a mazabar 001 da ke karamar hukumar Bakura yayin zaben maye gurbin.
Yayin da take gabatar da sakamakon mazabar, wakiliyar INEC mai kula da mazabar, A'isha Bawa, ta ce ta nemi ma'aikatan Sama ko kasa, ba ta gansu ba, sun bace bat bayan barkewar rikici.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng