2023: Yankin da dan takara zai fito bashi da muhimmanci, in ji Olawepo Hashim

2023: Yankin da dan takara zai fito bashi da muhimmanci, in ji Olawepo Hashim

- Olawepo-Hashim dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019 a jam'iyyar PT ya bayyana cewa karɓa-karɓa na iya cutar da Nigeria

- Ya bayyana cewa yanki ko addini da al'ada basu da muhimmanci, abu mafi muhimmanci shi ne nagarta

- Ya kuma bayyana cewa matukar mutum ya na da nagarta yan Najeriya za su zabe shi ko daga wane yanki ya fito

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Poeple's Trust (PT) a zaben 2019, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi gargadin cewa fitar da yankin da dan takara zai fito a zaben 2023 abu ne wanda bashi da muhimmanci.

Olawepo-Hashim, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce Najeriya tana bukatar shugaba na gari daga ko wanne yanki wanda a shirye ya ke kuma zai iya kawo ci gaba.

2023: Yankin da dan takara zai fito bashi da muhimmanci - Olawepo Hashim
2023: Yankin da dan takara zai fito bashi da muhimmanci - Olawepo Hashim. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Ya ce batun juya takara ko zabar yanki ba zai kawo ci gaba da hadin kai ba kuma ya karya ta batun zabar yankin dan takara, inda ya bayyana shi a matsayin yaudara da kuma abun da ke kawo cikas ga ci gaban kasa.

DUBA WANNAN: ASUU ta amince za ta janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba, inji Ngige

"Yanayin ya na cutar da hadin kai da ci gaban kasa, abu mafi muhimmanci, jujjuya shugabancin kasa abu ne da zai wargaza dunkulewar Najeriya guri daya ya Kuma kawo tunanin wace jiha ce ba ta da shugaban kasa.

"Najeriya ba zata zama kasa daya mai adalci ba idan wani dan kudu ya na gwada mulkin son kai a sama.

"Zai fi zama adalci idan aka raba mukamai ga kowacce jiha ba tare da la'akari da waye shugaban kasa ba."

KU KARANTA: Dakatar da ni da jam'iyya ta yi ya saba doka, tsohon mataimakin shugaban APC, Eta

Olawepo-Hashim, mashahurin dan kasuwa, ya ce mukamin shugaban kasa "ba sai anyi la'akari da al'ada, addini ko yankin da mutum ya fito ba, illa kawai a duba nagartar dan takara da kuma yadda zai iya kawo ci gaba."

Ya sake bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaban da zai hada kan yan kasar ya kuma samar da tsaro ya kuma mai da ita ta zamani.

Ya kuma bayyana cewa matukar mutum ya na da nagarta yan Najeriya za su zabe shi ko daga wane yanki ya fito.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel