ASUU ta amince za ta janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba, inji Ngige
- Gwamnatin tarayya ta yi martani game da kalaman shugaban kungiyar ASUU na cewa tayi alkawarin biyan dukkan albashinsu kafin su janye yajin aiki
- Ministan Kwadago, Chirs Ngige yace hasali ma sun cimma yarjejeniya a taronsu na karshe cewa ASUU zata janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba
- Yace bayan janye yajin aikin ne ministocin ilmi da kwadago za su nemi a janye dokar 'Ba bu aiki, babu albashi' sai an biya malaman sauran albashinsu
Gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin da shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya yi na cewa ta gaza cika alkawurran data dauka wa kungiiyar.
Gwamnatin ta ce babu shakka ta cikka alkawurran da ta dauka wa kungiyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Labari mai zafi: Buhari ya sallami shugaban Hukumar NDE, Ladan Argungu
Ministan Kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana cewa ASUU ta amince da cewa zata janye yajin aiki kafin ranar 9 ga watan Disamba a taron da suka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba duk da cewa ba rubutaccen yarjejeniya bane.
"Maganar gaskiya shine an 'cimma matsaya' a taron karshe da ASUU cewa zata janye yajin aiki kafin ranar 9 ga watan Disamban 2020, inda shi kuma Minista, ya amince cewa da zarar an janye yajin aikin zai nemi afuwar shugaban kasa a madadin ASUU don a biya su sauran albashinsu a ranar 9 ga watan Disamba ko kafin ranar," in ji Ngige.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwar da ofishin watsa labarai na Ngige ta fitar a ranar Talata mai taken, "Mun cika alkawurran da muka yi wa ASUU - FG".
Ogunyemi ya dora laifin cigaba da yajin aikin kan gwamnatin tarayya inda yace malaman ba zasu koma aji ba har sai an biya su sauran albashin da suke bi bashi.
KU KARANTA: Budurwa ta yi karar saurayinta bayan shafe shekara 8 suna soyayya ba amma ya ƙi aurenta
Sai dai Ngige ya ce karya ASUU ke yi kuma ba dai-dai bane ta dinga yi wa al'ummar kasa karyar cewa gwamnati ta ce zata biya dukkan albashin da suke bi bashi kafin su koma aiki inda yace sun biya dukkan bukatun da kungiyar ta gabatar a lokutan da aka yi yarjejeniya.
Ministan ya bada misalan wasu bukatun da kungiyar ta gabatar inda ya ce a makon da ta gabata FG ta kafa kwamitin tattaunawa kan yarjejeniyar shekarar 2009 karkashin jagorancin Farfesa Muzali.
A wani labrin daban, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata ya janye sharadin takara ga wanda suka shiga ko suke shirin shiga jam'iyyar.
Sharadin zai bada damar tsayawa takara a duk wata kujerar mulki ba tare da la'akari da dadewa a jam'iyyar ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka ga majalisa bayan kammala taron kwamitin kamar yada The Punch ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng