Yanzu-yanzu: An tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC da watanni 6

Yanzu-yanzu: An tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC da watanni 6

- Bayan tattauna na awanni, majalisar zartaswar APC ta yanke shawara

- Wannan sakamako bai yiwa wasu manya musamman Sanatoci dadi ba

- Buhari ya shawarci mabiya jam'iyyar su amince da hakan ko da basu ji dadi ba

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress APC, ta tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

TVC ta ruwaito cewa an tsawaita wa'adin zuwa ranar 30 ga Yunin 2021.

Hakan ya faru ne a ganawar gaggawan da majalisar tayi ranar Talata a fadar shugaban kasa dake Aso Villa Abuja.

An gudanar da taron ne karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Yanzu-yanzu: An tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC da watanni 6
Yanzu-yanzu: An tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC da watanni 6
Source: Twitter

KU DUBA: APC - NWC ta kalubalanci Shugaba Buhari, akwai yiwuwar a shigar da kara a gaban kotu

KU KARANTA: An wulakanta Shugaban APC, an hana shi magana a zaman NEC - Majiya

Mun kawo muku cewa majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yanzu haka na zaman gaggawa a fadar shugaban kasa, Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja.

Za ku tuna jam'iyyar ta shirya zaman a watan Nuwamba domin sanin abin yi kan shugabancinta amma bata samu dama ba.

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranci sauran mambobin majalisar zartaswar, har da shugaba Buhari wajen bude taron.

Sauran wadanda ke hallare a zaman sune shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da gwamnonin jam'iyyar, karkashin jagorancin shugabansu gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel