Yanzu-yanzu: An shiga zaman gaggawa na majalisar zartarwar jam'iyyar APC a Aso Rock

Yanzu-yanzu: An shiga zaman gaggawa na majalisar zartarwar jam'iyyar APC a Aso Rock

- Manya da masu fada a ji na jam'iyyar APC sun taru a fadar shugaban kasa

- Dukkan gwamnonin jam'iyyar sun taru dan yanke shawara mai muhimmanci

- An samu rabuwan kai tsakanin Sanatoci kan yunkurin tsawaita wa'adin kwamitin Buni

Majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yanzu haka na zaman gaggawa a fadar shugaban kasa, Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja.

Za ku tuna cewa jam'iyyar ta shirya zaman a watan Nuwamba domin sanin abin yi kan shugabancinta amma bata samu dama ba.

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranci sauran mambobin majalisar zartaswar, har da shugaba Buhari wajen bude taron.

Sauran wadanda ke hallare a zaman sune shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Hakazalika gwamnonin jam'iyyar, karkashin jagorancin shugabansu gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu na hallare.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

KU DUBA: AYCC ta bukaci Shugaban kasa yayi waje da Hafsun Soji da Babatunde Fashola

Yanzu-yanzu: An shiga zaman gaggawa na majalisar zartarwar jam'iyyar APC a Aso Rock
Yanzu-yanzu: An shiga zaman gaggawa na majalisar zartarwar jam'iyyar APC a Aso Rock Hoto: @Bashirahmaad
Asali: UGC

KU DUBA: An wulakanta Shugaban APC, an hana shi magana a zaman NEC - Majiya

Idan baku manta ba, a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, 2020 ne jam’iyyar APC ta kir taron majalisar koli ta NEC, inda aka sauke daukacin majalisar NWC mai alhakin gudanar da harkokin jam’iyya, wannan mataki ya bar baya da kura.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC ta jam’iyyar APC da aka ruguza a wajen taron NEC sun ce su na tuntubar Lauyoyi da masu ruwa da tsaki domin yanke shawara game da matakin da za su dauka.

Majalisar NEC ta zabi Alhaji Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa a matsayin shugaban rikon kwarya wanda zai gudanar da sabon zabe.

Tsofaffin shugabannin jam’iyyar ta APC a majalisar Adams Oshiomhole, wanda kotu ta dakatar, sun nuna cewa ba su gamsu da wannan mataki da manyan jam’iyyar su ka dauka a taron NEC ba.

Victor Giadom ne ya kira wannan taro, wanda ‘ya ‘yan NWC su ka ki halarta, kuma su ka ce zaman da aka yi ya sabawa doka domin ya ci karo da sashe na 25(B) na tsarin mulkin jam’iyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel