An wulakanta Shugaban APC, an hana shi magana a zaman NEC - Majiya

An wulakanta Shugaban APC, an hana shi magana a zaman NEC - Majiya

A lokacin da Victor Giadom ya ke tunanin cewa ya samu damar darewa kan kujerar shugaban jam’iyyar APC bayan mubaya’ar shugaban kasa, sai kuma daga baya labari ya canza.

Yayin da aka shiga taron NEC na jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada shawarar a ruguza majalisar NWC, wanda hakan ya kawo karshen shugabanni na kasa.

Victor Giadom wanda ya ke ikirarin cewa shi ne sabon shugaban jam’iyyar APC bayan kotu ta dakatar da Adams Ohiomhole, ya sha kunya a wajen wannan taro da aka gudanar jiya.

Jaridar The Nation ta ce Victor Giadom ya yi mamaki da jin cewa Mai Bala Muni zai rike APC a matsayin shugaban rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben shugabanni.

Wata majiyar jaridar da ta samu labarin abin da ya faru a taron na NEC, ta ce Giadom ya yi mamaki da aka hana shi yin magana gaba daya a taron, da zarar ya yunkuro sai a dakatar da shi.

A lokacin da Victor Giadom ya yi kokarin tsoma bakinsa a taron, sai shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya yi wuf ya taka masa burki, ya bukaci ya yi tsit.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya sa aka ruguza Majalisar Shugabannin APC

An wulakanta Shugaban APC, an hana shi magana a zaman NEC - Majiya
Victor Giadom Hoto: APC
Asali: UGC

Femi Gbajabiamila ya shaidawa mataimakin sakataren jam’iyyar cewa wa’adinsa ya kare a matsayin shugaban APC na rikon kwarya, don haka ya ce bai da hurumin da zai saka baki.

Bayan an fito taron, Victor Giadom, ya yi magana a shafinsa na Twitter, ya ce bayan ruguza majalisar NWC, babu wanda ya yi nasara, haka kuma babu wanda zai ce ya yi rashi.

Ya ce: “Matsayata a kan taron APC NEC na yau: Na fada a baya cewa matakin da majalisar NEC za ta dauka zai yi galaba. Na kuma yi alkawarin cewa zan goyi bayan wannan mataki.”

“Shugaban kasa Buhari a jawabinsa ya ce dole a ruguza majalisar NWC, a kuma nada kwamtin da zai shirya sabon zaben shugabannin jam’iyya idan ana so a koma hanyar nasara”

Jawabin Giadom ya nuna akasin rahoton, ya nuna ya na tare da matakin da Shugaban kasa da NEC su ka dauka, inda a karshe shi da sauran abokan hamayya su ka rasa kujera.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng