Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna

Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna

- Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa ta fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha domin tabbatar da tsaron jihar

- Kwamishinan kananan hukumomi a Kaduna, Ja'afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da 'yan sandan jihar

- Sanata Uba Sani ya ce ya na aiki a kan kudirin da zai bayar da damar samun 'yan sandan tarayya da na jihohi

Gwamnatin Kaduna ta fara tantance matasa a kokarinta na shirin fara aiki da 'yan sandan jiha domin inganta tsaro a jihar, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Uba Sani, Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, shine ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani taro da ma su ruwa da tsaki a sha'anin tsaro.

Hadiza Balarabe, mukaddashiyar gwamnan jihar Kaduna, ita ce ta jagoranci taron da aka yi a Kaduna.

Taron ya samu halartar 'yan majalisar jiha da na tarraya daga Kaduna, shugabannin kananan hukumomi 15 da ke arewacin Kaduna, da hakimai.

KARANTA: A Villa ake babban iskanci kuma Buhari ne jagora: Aisha ta mayar da martani kan gargadin Buhari

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron, Sanata Sani ya bayyana cewa ya na aiki a kan kudirin neman sake fasalin 'yan sanda domin fuskantar kalubalen tsaro da kasa ke fama da shi.

Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna
Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna @Thecable
Asali: Twitter

A cewarsa, idan kudirin ya samu karbuwa a majalisa, za'a kirkiri 'yan sandan jiha.

"Ina aiki a kan wani kudiri da zai sauya fasalin aiki da kunshin rundunar 'yan sanda, hakan zai bayar da damar samun 'yan sandan jiha da na tarayya.

"Mu na son kawo karshen kalubalen tsaro a jihar Kaduna da Nigeria baki daya.

KARANTA: An kama Idris mai wankin mota a hanyarsa ta zuwa ya siyar da galleliyar motar kwastoma

"Za mu yi aiki da jama'a wajen magance matsalar tsaro a jiha, ta hanyar aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin siyasa. Gwamnan jiharmu a shirye ya ke tsaf domin kawo karshen matsalar tsaro," a cewar Uba Sani.

A nasa bangaren, kwamishinan kananan hukumomin jihar Kaduna, Ja'afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da 'yan sandan jiha.

A cikin watan Mayu na shekarar 2019 ne babba sifeton rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya bashi izinin fara tsara hanyoyin samar da 'yan sandan jiha a fadin Nigeria.

A cikin watan Agusta, gwamnatin tarayya ta amince da fitar da biliyan N13.3 domin kaddamar da tsarin 'yan sandan jihohi a Nigeria.

A ranar Talata, 1 ga watan Disamba, 2020, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaba Buhari ya bayar da umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukakawa jama'a kalubalen sufuri da rage musu radadin kara farashin man fetur.

Buhari ya mika sakon godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa abin da ya kira 'hakurin da suka nuna' dangane da kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta

Kazalika, ya godewa mambobin kungiyar kwadago bisa fahimta da dattakon da kuma kishin kasa da suka nuna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel