A villa ake iskanci na gaske: Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari
- Aisha Yesufu, 'yar gwagwarmaya kuma jagorar zanga-zangar EndSARS, ta mayar da martani mai yaji ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya yi gargadin cewa zai magance duk wani salo na iskanci kuma ta kowacce siga aka bullo da shi
- A martanin da ta yi akan gargadin shugaba Buhari, Aisha ta ce a fadar shugaban kasa ake iskanci na gaske
Fitacciyar 'yar gwagwarmaya kuma daya daga cikin jagororin zanga-zangar EndSARS, Aisha Yesufu, ta mayar da martani a kan gargadin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa ma su zanga-zanagar EndSARS a ranar Litinin.
Shugaba Buhari ya yi gargadin ne a yayin da wasu matasa su ka kara fitowa domin sake farfado da zanga-zangar EndSARS a karo na biyu a Lagos da Osun. Buhari ya ci al washin yin maganin duk wani salon iskanci.
A cikin wani martani da ta fitar jim kadan bayan gargadin da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na tuwita, Aisha ta bayyana shugaba Buhari a matsayin matsoraci tare da bayyana cewa a fadar shugaban kasa (Aso-Villa) ake aikata babban iskanci.
KARANTA: Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyon bayan takarar Tinubu a 2023
"An nemi matsoracin an rasa a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe manoma 78 saboda kawai an kama daya daga cikinsu.
"A Aso Villa ake iskanci na gaske kuma shugaba Buhari ke jagorantarsa! kamar yadda Aisha ta wallafa a martanin da ta wallafa a kan sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
KARANTA: Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi
Legit.ng Hausa, a kwanakin baya, ta rawaito cewa Dr.Chinonso Egemba wanda aka fi sani da Aproko Doctor da ƴar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, sun maida martani kan ƙarar da Kenechukwu Okeke, ya shigar dasu akan marawa masu zanga-zangar EndSARS baya.
Rahotanni sun bayyana cewa Okeke ya shigar da ƙarar masu goyawa zanga-zangar EndSARS baya a babbar kotun tarayya dake Abuja.
Okeke lokacin da yake bayyana dalilin shigar da ƙarar yace yayi haka ne don wanzuwar tsaro,kare al'umma da kuma dawo da lumana a cikin al-umma.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng