Saukaka Sufuri: Buhari ya bayar da umarnin sakin manyan motocin alfarma
- A cikin watan Satumba ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta raba sabbin manyan motocin sufuri a fadin kasar na
- A cewar gwamnatin tarayya, yin hakan zai saukaka kalubalen sufuri da kuma saukaka rayuwa sakamakon tashin farashin mai
- A yayin wani taro da shugaba Buhari ya jagoranta a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, ya bayar da umarnin sakin motocin
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya bayar da umarnin sakin sabbin manyan motocin alfarma domin saukakawa jama'a kalubalen sufuri da rage musu radadin kara farashin man fetur.
Buhari ya mika sakon godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa abin da ya kira 'hakurin da suka nuna' dangane da kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta
Kazalika, ya godewa mambobin kungiyar kwadago bisa fahimta da dattakon da kuma kishin kasa da suka nuna.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci wasu taro ta yanar gizo daga fadarsa, Villa, Abuja, kamar yadda kakakinsa, Femi Adesina, ya bayyana.
KARANTA: Garba Shehu: An yi min mummunar fassara, ba'a fahimci kalamaina da kyau ba a kan kisan manoma
Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su rungumi amfani da sinadarin gas amadadin fetur.
A ranar Juma'a, 11 ga watan Satumba, ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin raba motoci 2000 domin saukaka sufuri a fadin tarayya da rage radadin tashin farashin man fetur, musamman ga mazauna karkara.
Ministan harkoki na musamman, George Akume, ya bayyana hakan a Abuja a taron tattaunawar da ya yi da yan kungiyoyin hadaka da masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri.
A cewarsa, shirin zai gudana ne tsakanin ma'aikatarsa, ma'aikatar aikin noma da raya karkara da kuma wasu hukumomin gwamnati.
Akume ya ce an yanke shawarar bi ta hannun kungiyoyin hadaka ne saboda tabbatar da aiwatar da shirin, maimakon baiwa wasu daidaikun mutane bashi, wanda hakan zai jinkirta aiwatar da aikin.
"Abinda muka lura shine, idan aka baiwa daidaikun mutane bashi, dawowa da shi na matukar wuya, amma idan akayi da kungiyoyin hadaka, abin zai fi saukin lura."
Akume yace "Manufar wannan shiri shine tabbatar da cewa mutanen karkara na samun saukin sufuri, yanzu da aka samu tashin farashin man fetur."
Ko a kwanakin baya, Legit.ng Hausa ta rawaito ministar kudi, Zainab Ahmed, na dora alhakin hauhawar farashin kayan masarufi da tsadar kudin mota.
A cewar Zainab, gwamnatin tarayya za ta samar da hanyar saukakka sufuri domin shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi.
Batun sakin sabbin motocin na zuwa cikin kasa da sati biyu da kalaman minista Zainab a kan saukaka wa 'yan sufuri.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng