Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa dakarun soji hari, sun kashe sojojin ruwa 2
- Miyagun 'yan bindiga sun kai wa dakarun soji hari a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi
- Kamar yadda shugaban karamar hukumar ya tabbatar, soji 2 sun rasu, wasu 2 sun jigata
- Ya fitar da sanarwan ne ta wata takarda daga ofishin mai bashi shawara na musamman
Wasu 'yan bindiga a ranar Laraba da yammaci sun kai wa dakarun soji hari a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi inda suka kashe sojin ruwa biyu.
Jaridar Tribune Online ta tabbatar da cewa an kai wa sojin hari wurin karfe 7 na yammacin ranar Laraba a Okene yayin da suke shirin fara aiki.
Shugaban karamar hukumar Okene, Abdulmumin Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.
KU KARANTA: Duba cikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan mai AC, wurin caji da bandaki kayatacce
Takardar wacce ya fitar ta ofishin mai bashi shawara ta musamman, ya ce sojin ruwan biyar ne kuma za su fara aiki kenan aka kai musu harin.
"An tabbatar da kisan wasu soji biyu yayin da biyu suka jigata. Daya ya tsere ba tare da samun wani rauni ba."
KU KARANTA: Rashin tsaro: Ba zan taba neman sasanci ko ciniki da 'yan bindiga ba, Yahaya Bello
A wani labari na daban, Reno Omokri, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sha alwashin bai wa Garba Shehu kyautar $20,000 idan har ya kwana a Koshobe ko Kware.
Omokri ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.
Ya ce ya saka wannan kudin ne saboda Shehu ya ce Buhari ya tabbatar da cewa ya inganta tsaron kasar nan. Omokri ya nada Dele Momodu a matsayin shaida.
Koshebe da Kware wurare ne a jihohin Borno da Zamfara kuma an tabbatar da cewa suna cikin wurare da rashin tsaro ya tsananta kuma hare-haren 'yan Boko Haram da 'yan Bindiga ya yi kamari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng