An yabawa Zulum bayan bidiyo ya nuna yadda aka birne manoma tare da shi (Kalli bidiyon)

An yabawa Zulum bayan bidiyo ya nuna yadda aka birne manoma tare da shi (Kalli bidiyon)

- Masu ta'aziyya a gida da waje sun yi alhinin kisan manoma 47 a Zabarmari, jihar Borno

- Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kisan wadannan manoma

- Yau mako daya da rashin wadannan mutane da aka raba iyalansu

Kisan akalla manoma akalla 47 a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, ya sake jaddada kiran da mutane ke yi na shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro.

Hakazalika wasu sun yi kira da shugaban kasa yayi murabus saboda tabarbarewan tsaro.

Amma yayinda jama'a ke cigaba da tsokaci kan lamari, gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sha ruwan addu'o'i bisa irin abubuwan da yayi lokacin jana'izar mamatan.

A bidiyon da ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, an ga gwamnan cikin jama'a ana birne mamatan tare da shi duk da matsayinsa na gwamna.

An ga Zulum yana kwaba kasa yana zubawa kan kabarin mamatan.

Gwamnan ya cika da hawaye da damuwa kuma yayi maganganu masu ratsa zuciya kan abinda ya kamata gwamnatin tarayya tayi don kare rayukan jama'a a kasar nan.

An yabawa Zulum bayan bidiyo ya nuna yadda aka birne manoma tare da shi (Kalli bidiyon)
An yabawa Zulum bayan bidiyo ya nuna yadda aka birne manoma tare da shi (Kalli bidiyon)
Source: Twitter

KU KARANTA: Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari

Kalli bidiyon:

KU DUBA: Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina

Mun kawo muku cewa Iyalan kowanne cikin manoma 48 da aka kashe a gonan shinkafa a jihar Borno ya samu kudi N600,000 daga hannun gwamnatin jihar Borno.

Hakazalika sun samu buhuhunan kayan abinci daga kwamitin da gwamna Babagana Umara Zulum ya nada domin raba kayan tallafin.

Kudin ya samu ne daga hannun Kungiyar gwamnonin Arewa, da suka bada gudunmuwan N20m, yayinda hukumar cigaban Arewa maso gabas NEDC ta bada N5m, rahoton Thisday.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel