Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari

Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari

- Za'a yi zaben yan majalisun jiha domin maye gibin wadanda suka mutu

- Cikin zabukan da za'ayi a jihohi daban-daban a fadin tarayya, akwai daya a jihar Zamfara

- Yan takara 14 zaku kara gobe domin lashe kujerar dan majalisan mazabar Bakura

Gwamnan jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle, ranar Juma'a ya gargadi gwamnonin APC biyar da Sanatoci bakwai da tsohon gwamna Yari ya gayyata su nisanta kansu daga jiharsa.

Matawalle ya bayyana hakan yayinda ake shirin zaben yan majalisa ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya yi wannan gargadi ne bayan duba dukiyan da yan daba suka lalata yayin yakin neman zabe ranar Alhamis.

"Idan tsohon gwamna Yari dan halas ne kuma haifaffen iyayensa, ya fadawa mutanensa su nisanta kansu daga zaben ranar Asabar a jihar. Kuma idan ya cika jarumi, ya fuskanceni. Zan lallasa shi," yayi gargadi.

"Ya gayyaci gwamnoni biyar, Sanatoci bakwai da yan majalisa gooma, har da Ministan harkokin yan sanda Zamfara don tayashi lashe zabe."

"Irinsu Ministan harkokin yan sanda batawa shugaba Muhammadu Buhari suna sukeyi."

"Ya gayyato yan daba suna tayar da hankulan mutanenmu har aka kashe biyu kuma aka lalata wuraren yakin neman zabenmu da dukiyoyin mutane.

"Ina gargadin wadannan gwamnoni cewa jihar Zamfara daban take kuma su cire kansu daga lamuranmu. Su bari mutane su zabi wanda suke so."

KU KARANTA: Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina

Amma, mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressive Congress APC na jihar, Alhaji Sani Gwamna Mayanchi, ya yi watsi da wadannan zarge-zarge na gwamnan.

Ya ce basu kaiwa kowa hari ba kuma jami'an tsaro shaidu ne.

Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari
Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari Credit: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Kawai gwadawa nayi, Matashi ya debi amfanin noman da yayi a harabar gidansa

A bangare guda, Jagoran APC a kasar Yarbawa, Bola Ahmed Tinubu da wasu kusoshin APC sun kawo karshen rikicin cikin gidan da su ke fama da shi a jihar Osun.

Tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, sun yi wata gana wa da jiga-jigan APC mai mulki a Osun.

Bisi Akande da Bola Ahmed Tinubu sun sa labule ne da gwamna mai-ci Adegboyega Oyetola da mai gidansa, Rauf Aregbesola.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel