Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe

Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe

- Gwamnatin Borno ta raba kayan rage radadi ga iyalan mutanen da aka kashe karhsen mako da ya gabata

- Gwamnonin Arewa sun bada gudunmuwa domin rabawa wadannan iyalai

- Hakazalika Shugaba Buhari ya aika kayan abinci domin raba musu

Iyalan kowanne cikin manoma 48 da aka kashe a gonan shinkafa a jihar Borno ya samu kudi N600,000 daga hannun gwamnatin jihar Borno.

Hakazalika sun samu buhuhunan kayan abinci daga kwamitin da gwamna Babagana Umara Zulum ya nada domin raba kayan tallafin.

Kudin ya samu ne daga hannun Kungiyar gwamnonin Arewa, da suka bada gudunmuwan N20m, yayinda hukumar cigaban Arewa maso gabas NEDC ta bada N5m, rahoton Thisday.

Kwamitin karkashin jagorancin kwamishanan matasa da wasanni, Saina Buba, ta raba kudaden ranan Alhamis a Zabarmari.

Sauran mambobin kwamitin rabon sune dan majalisar wakilai mai wakiltan Jere, yan majalisun jiha dake wakiltan Jere biyu, masu baiwa gwamna shawara biyu, da kuma zababben shugaban karamar hukumar Jere.

Buba ya bayyana cewa N600,000 da aka basu da kayan abinci ba diyyan mamatansu bane, illa kawai don a rage musu radadin rashin da sukayi.

KU KARANTA: Matsalar Tsaron Najeriya ta fi ƙarfin Soja,inji Gwamnati

Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe
Gwamnatin Borno ta biya N600,000 ga kowanne cikin iyalan manoma 48 da aka kashe Hoto: thecableng
Source: Twitter

KU DUBA: Saboda kokarin Buhari, yan Boko Haram sun daina karban haraji hannun mutane

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin raba kayan tallafi ga iyalan da kisan manoma 44 da yan ta'addan Boko Haram suka hallaka a jihar Borno.

Ministar tallafi da jin dadin jama'a, Sadiya Farouk, ta wanzar da umurnin ranar Laraba, 2 ga Disamba, 2020.

Kayan da aka rabamusu sun hada da: Buhun shinkafan 12.5kg 13,000; buhun masara 12.5kg 13,000; buhun wake 25kg 13,000; galolin man gyada 1,300; kwalayen dandano 2,116; kwalayen tumatur na gwangwani 1,083; da jakunan gishiri 650.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel