Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur

Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur

- Mashood Adisa Ajala, mutum ne mai dumbin tarihi cike da burgewa da ban sha'awa

- Shine mutumin da ya zagaye kasashe 87 na turawa a babur inda yayi suna, kuma ya samu daukaka

- Ya kai kololuwa a rayuwarsa, sai dai daga baya ya mutu cikin mawuyacin hali, har iyalansa suka guje shi

An haifi Mashood Adisa Ajala a Ghana, shekarar 1930. Yana da kanni da yayyi 24, mahaifinsa yana da mata 4. Bayan haihuwar Ajala, iyayensa suka koma Najeriya, inda yayi karatunsa a Baptist Academy da ke Legas da Ibadan Boys' High School.

Bayan Olabisi ya kai shekaru 18 da haihuwa, ya tafi jami'ar Chicago, don yayi karatun likitanci. Yana da burin zama likita don ya koma Najeriya ya taimaki mutane, inda bokaye da masu magungunan gargajiya suka fi kamari.

Bayan nan sha'awar tukin keken tsere ta shiga ransa, inda ya fara tseren a 1952, lokacin yana da shekaru 22 a duniya.

A tseren yana yawon 2,280 miles a keke. Lokacin da ya isa Amurka, yana da burin nuna musu cewa bakaken fata ba sa yawo tsirara ko kuma amfani da fatun dabbobi. Duk inda yaje, yana sanya sutturu irin na gargajiya.

KU KARANTA: Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya

Nan da nan labarai suka fara yawo a kan wani dan Afirika da ke yawo da sutturun gargajiya a keke, Ajala ya zama sananne.

Har a gidan talabijin da jaridu ake wallafa hotunansa da labaransa, inda ake kwatanta shi a matsayin mutum mai kwarjini. Bayan nan ne yayi digiri a Psychology a jami'ar Columbia, Ajala ya tara ilimi mai yawa.

Har a fina-finai aka tsiri sanya Ajala, a fim dinsa na farko mai suna "White Witch Doctor", ya samu $300 duk Mako. Sannan duk fina-finansa da sutturu irin na Afirika ya ke yinsu.

Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur
Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur. Hoto daga twmagazine.net
Asali: UGC

Ajala ya zagaye kasashe 87 a babur dinsa, a nan ne ya san manyan 'yan siyasan kasashe kamar Gamal Abdul Nasser na Egypt, Jawarhalar Nehru na India, Mohammad Reza Shah Pahlavi na Iran, Ronald Reagan na Amurka, Abubakar Tafawa Balewa na Najeriya da sauransu.

KU KARANTA: Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure

Sai dai ya fara rayuwa mai dadi amma daga baya ya shiga cikin masifun rayuwa. Ya fara fuskantar kalubale bayan wata ma'aikaciyar jinya a Chicago ta ce ta haifa masa jariri a 1953, wanda ta sanya wa suna Oladipupo.

Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur
Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur. Hoto daga autoreportng.com
Asali: UGC

Olabisi ya ki amincewa da haifar yaron sai har an tabbatar da dansa ne ta hanyar gwajin asibiti, kuma ta amince amma sai ya tsere.

Bayan nan ne kotu ta yanke masa hukuncin biyan $10 duk sati. A wannan shekarar aka kama shi da laifin amfani da takardar banki ta bogi da kuma sata.

Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur
Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur. Hoto daga twitter.com
Asali: UGC

Duk da ya musa laifin, amma an yanke masa shekara 1 a gidan gyaran hali. Bayan ya fito, aka kara kama shi da laifin keta dokar dalibai, inda ya kamata yayi karatu a Santa Monica Junior College amma ba can yaje ba. Bayan ya wuni a gidan rediyo yana bukatar a yi masa adalci.

Ajala ya koma Amurka tare da matarsa Hermine Aileen a 1954, duk da aurensu bai yi wani karko ba, inda tayi ta zargin yana ha'intarta.

Ya kara aure bayan 'yan watanni, inda ya auri wata jarumar finafinan turai, Joan. Daga baya ya koma Najeriya, saboda daukakarsa tayi kasa. Ya nemi hayar wani gida a Adeniran St. Bariga inda ya zauna tare da yaransa.

Bayan ciwo ya kama shi, kusan duk yaransa sun guje shi, ban da dansa Olaolu mai shekaru 20 da diyarsa Bolanle mai shekaru 17 a lokacin.

Ya mutu a babban asibiti da ke Ikeja a ranar 2 ga watan Fabrairun 1999 a cikin mawuyacin hali.

A wani labari na daban, a ranar Talata, kungiyoyin hadin kan arewa sun ce kashe-kashen da ake yi a arewacin Najeriya alama ce da ke nuna kuri'un da 'yan arewa suka kada wa shugaba Muhammadu Buhari a 2015 da 2019, sun zama asara.

A cewarsu, wannan harin da aka kai wa manoman jihar Borno, wadanda basu ji ba basu gani ba, alama ce wacce ta nuna cewa 'yan arewa sun yi kuskuren zabar Buhari.

A Wata takarda da kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman ya gabatar, ya ce yanzu Buhari ya zurawa 'yan arewa ido har rashin tsaro, talauci da mulkin kama-karya yayi ajalinsu gabadaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel