'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi

'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi

- A ranar Talata, kungiyoyin hadin kan arewa sun furta zafafan kalamai a kan Shugaba Buhari

- Sun ce Buhari ya zura ido yadda yunwa, fatara, rashin tsaro da mulkin kama karya zai kashe 'yan arewa

- A cewarsu, babban kuskuren da 'yan arewa suka yi a 2015 da 2019 shine zazzagawa Buhari ruwan kuri'u

A ranar Talata, kungiyoyin hadin kan arewa sun ce kashe-kashen da ake yi a arewacin Najeriya alama ce da ke nuna kuri'un da 'yan arewa suka kada wa shugaba Muhammadu Buhari a 2015 da 2019, sun zama asara.

A cewarsu, wannan harin da aka kai wa manoman jihar Borno, wadanda basu ji ba basu gani ba, alama ce wacce ta nuna cewa 'yan arewa sun yi kuskuren zabar Buhari, Daily Trust ta wallafa.

A Wata takarda da kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman ya gabatar, ya ce yanzu Buhari ya zurawa 'yan arewa ido har rashin tsaro, talauci da mulkin kama-karya yayi ajalinsu gabadaya.

KU KARANTA: Matashin da ke samun 20,000 a wata ya siya wa budurwarsa abincin 4,500

'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi
'Yan arewa sun yi gagarumar asara da suka saka wa Buhari kuri'u, Kungiyoyi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ina tsaka da bacci yake watsa min ruwa saboda na hana shi hakkinsa, Matar aure

A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon.

A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da 'yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.

A cewarsa: "Akwai mutanen da za su tuna lokacin da Janar Gowon ya bar Najeriya da rabin kudin CBN, kuma ya tare a Landan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng