Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya

Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya

- Majalisar dattawa ta kira wani babban dan majalisar Birtaniya

- Dan majalisar ya yi suka ga tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon

- A ranar 23 ga watan Nuwamba, Tugendhat ya yi wa Gowon kazafin sata

Majalisar dattawa ta kira wani babban kwamishinan Birtaniya zuwa Najeriya a kan wani tsokaci da wani dan majalisar Birtaniya, Tom Tugendhat yayi a kan tsohon shugaban kasan Najeriya, Yakubu Gowon, Thisday ta wallafa.

A ranar 23 ga watan Nuwamba, ana tsaka da wata muhawara a kan majalisar UK na korafin da 'yan Najeriya suka yi a kan hukunta jami'an tsaron da suke da hannu a kan kashe-kashen Lekki Toll Gate, ya zargi Gowon da kwashe rabin kudin CBN ya gudu dasu lokacin da ya bace.

A cewarsa: "Akwai mutanen da za su tuna lokacin da Janar Gowon ya bar Najeriya da rabin kudin CBN, kuma ya tare a Landan."

Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya
Gowon: Majalisar wakilai ta yi kiran gaggawa ga jakadan Birtaniya a Najeriya. Hoto daga @Thisday
Source: Twitter

KU KARANTA: Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata

Amma bayan komawarsu majalisar ranar Talata, Tugendhat ya bukaci majalisar ta bayar da hakuri ga Gowon da sauran 'yan Najeriya.

Majalisar wakilai ta tilasta kwamitinta na harkokin kasashen ketare da ta shiga ta tattauna da kwamitin harkokin kasar waje na majalisar Birtaniya a kan wannan tsokacin.

Hon Yusuf Gagdi ya ce wannan kazafin da dan majalisar Birtaniya yayi ba shi da tushe balle makama. Sannan ya ce wannan kazafin zai iya kawo tashin hankali da rikici, wanda zai iya janyo cece-kuce a kasa.

KU KARANTA: Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata

A wani labari na daban, Saudiyya ta nuna alhininta a kan kisan manoman shinkafa da ake zargin 'yan Boko Haram sun yi a Borno.

Saudiyya ta wallafa wannan sakon a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta nuna alhininta a kan yadda maharan suke kai wa fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba fargaba.

Kamar yadda ta wallafa, "Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe, da mutanen jihar, gwamnati da al'ummar Najeriya gaba daya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel