An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi

An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi

- An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi

- An yi rashin sa'a yaron ya rasa ransa sakamakon jefar da shi da tayi yayin gudu

Kotun Majistare ta IV a Birnin Kebbi, ta bada umurnin garkame wata mata mai suna, Patricia Nebochi, a gidan yarin Argungun kan laifin satan dan jariri a jihar.

Matar, mai zama a garin Tambuwal ta saci jaririn ne a asibiti Aisha Muhammadu Buhari dake garin Jega, Daily Trust ta ruwaito.

Miss Nebochi, ta saci yaron wata mata mai suna Fatimah Galbi, yar garin Galbi, karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi.

Lauyan yan sanda, Sifeto Muttari, ya bayyanawa kotu cewa "a ranar 21 ga Nuwamba, 21, 2020, misalin karfe 4 na yamma, wani mai gadi a asibiti ya damke matar da ta saci jaririn."

Mai gadin mai suna Mati yace, "lokacin da ake kokarin kamata, ta jefar da jaririn don ta gudu, kuma sakamakon haka jaririn ya mutu".

Lauyan yace ana gurfanar da ita ne kan laifi satan mutum da kisan kai.

Saboda haka ya bukaci kotu ta garkame ta a gidan kurkuku kafin hukumar yan sanda ta kammala bincike.

Alkalin kotun, Zainab Bello Suru, ta bada umurnin a tsareta a kotun yayinda ta dage karar zuwa ranar 5 ga Junairu, 2021.

KU KARANTA: Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana

An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi
An garkame wata matar 'yar kabilar Igbo da ta saci jariri a jihar Kebbi
Asali: UGC

KU KARANTA: Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa

A wani labarin kuwa, wani matashi ya rasa ransa a garin Calabar yayinda ya bukaci budurwarsa ta harbeshi da bindiga domin gwada sihhancin maganin bindigan da ya sha.

Matashin wanda akafi sani da 'Email' ya mutu har lahira bayan harbin da tayi masa.

Vanguard ta ruwaito cewa mamacin ya kasance dan kungiyar daba kuma mai sayar da kwayoyi na tare da abokansa ne lokacin da abin ya faru a gidansa dake Nelson Mandela street, Calabar South.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel