Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana

Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana

- Abubakar Shekau, shugaban tsagin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, ya saki sabon faifan bidiyo a ranar Talata

- A cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna uku, Shekau ya fadi dalilin kungiyarsa na aikata kisan gilla a kan fararen hula

- Kazalika, Shekau ya yi barazana da gargadi ga jama'ar jihar Borno a kan su guji bawa sojoji bayanai idan suna son zaman lafiya

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya tabbatar da cewa kungiyarsa ce ta kai hari tare da kashe manoman shinkafa a Kwashebe, Zabarmari, a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno.

Shekau ya yi barazanar cewa zai hukunta duk wanda ya bawa rundunar soji bayanai a kan kungiyarsa.

Legit.ng Hausa ta saurari faifan bidiyon Shekau mai tsawon mintuna uku, inda ya yi magana a kan cewa kungiyarsa ta hallaka manoma 78 saboda sun kama daya daga cikin mayakansa sun mika shi hannun sojoji.

"Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai, mu na miƙa godiya ga ubangijin bayi bisa ni'imar da ya yi mana.

"Bayan haka. Mune Jama'atu Ahlussunnati L'idda'awati wal Jihad Wanda suke ƙarƙashin jagorancin Imam Sheik Abubakar Shekau Hafizahullah.

"Mu na tura saƙo zuwa ga al'ummar Najeriya, lallai abin da ya faru a gefen Maiduguri a kwanan nan, waɗanda ake surutai akai, musamman a unguwar Zabarmari, to wannan aikin mune muka yi.

Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana
Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana @Daily_trust
Source: Twitter

"Kuma aikin da akayi a Angom shima mu ne muka yi.

"To saboda haka ku sani, kuna tsammanin cewa ku kama ɗan uwanmu, ku miƙawa soja, sannan ku zauna lafiya, shin kuna tsammanin abin da kuka yi wa ɗan uwanmu Allah zai manta ne.

"Saboda haka saƙonmu na biyu kuma zuwa gareku shine ku tuba! Ku tuba!! Tubanku shi yafi mana alheri akan kisanku, ma'ana ba kisanku muke buƙata ba, Ku tuba ku bi addinin Allah shine bukatar mu.

"Saboda haka ne muke yin da'awa kuma shine burinmu sai wanda yaƙi sannan zamu yaƙe shi.

"Wanda ya tuba ɗan uwanmu ne, za mu karɓeshi hannu bibiyu ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda muka karɓi wasu bayan tuban da wasu sukayi.

"Kuma saƙo na uku shine gun waɗanda suka kangare, suka cije akan abin da suke kai, ma'ana na kama ƴan'uwanmu su miƙawa soja ko kuma su yi cune a kama su da dai sauransu.

"Ku sani abin da ya samu waɗannan, abin da ya samu mutanenku, a yanzu to kuma zai sameku matuƙar in baku daina ba, kuma idan kuna ganin wannan zai kawo muku cigaba ku cigaba ku gani, mu kuma ba zamu daina ba, wannan shine alƙawarin da muka ɗauka, kuma Allah ta'ala zai bamu Nasara," a cewarsa.

Legit.ng Hausa ta rawaito yadda ba tare da girmama rai ko rayuwar dan adam ba, mayakan Boko Haram suka daure manoman, suka yankasu, sannan suka kone gonakinsu.

Malam Abubakar Yunusa, ɗaya ne daga cikin waɗanda harin Zabarmari ya shafa, Uba ne da ya rasa ƴaƴansa biyu a mummunan harin da aka kai a garin Zabarmari, jihar Borno, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Ya ce an kama shi da ƴa'ƴansa biyu sannan aka yi musu yankan rago akan idonsa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel