Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa

Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa

- Majalisar dattawa ta mika bukatu bakwai ga shugaba Buhari na shawo kan lamarin tsaro

- Na farko ciki shine ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya

- Sanata Babba Kaita ya yi alhinin rashin amfanin makudan kudaden da ake baiwa Sojoji kowace shekara

Sanata mai wakiltan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba-Kaita, ya yi Alla-wadai da hare-haren da ake kaiwa sassan kasar nan.

Yayin jawabi a zauren majalisa ranar Talata, Kaita ya ce abubuwan da gwamnatin nan ke yi basu haifar da 'da mai ido ba har yanzu.

Ya ce idan ba'a dau mataki ba, yan bindiga zasu kwace kasar.

Dan majalisan wanda ke wakiltan mazabar Buhari a majalisar dattawa, ya ce wajibi ne a binciki shugabannin Sojoji kan makudan kudaden da ake basu domin yakar ta'addanci.

"Lokacin fadin gaskiya yayi. Ba bu dan Najeriyan da zai cigaba da yarda da abinda ke faruwa. Ba zai yiwu mu cigaba da jimamin mutuwar mutane ba kullum, " yace.

"Ba zamu amince da bayanan wadanda ya kamata suyi abinda ya dace ba duk lokacin da aka kai hari. Idan da gaske Garba Shehu ya fadi haka, to gaskiya akwai rashin tunani."

"Ta yaya za'a kashe mutanen da suka je gonakinsu noma duk da talaucin da ake ciki kuma su rasa rayukansu amma wani yace basu nemi izini ba. Ba'a girban kayan gona a rana daya, muna girba na tsawon lokaci."

KU DUBA: Budurwa ta kashe saurayinta bayan ya bukaci ta harbeshi don gwada maganin bindiga

Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa
Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa Hoto: @babbahmad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon bidiyo: Shekau ya fadi dalilin kisan manoma a Zabarmari, ya yi wa fararen hula barazana

A bangare guda, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, inda ya shawarcesa da ya fatattaki kaf ministoci da hadimansa don sun gaza yin ayyukansu yadda ya kamata, The Nation ta wallafa.

Ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Lafia, lokacin da ya kai gaisuwa ga Gwamna Abdullahi Sule a gidan gwamnati da iyalansa bisa rashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Mr. Philip Tatari Shekwo wanda 'yan bindiga suka kashe.

A cewarsa, "Ya kamata shugaba Buhari ta fatattaki kaf mutanen da ya dauka don su yi wa kasar nan aiki, don sun kasa aiwatar da komai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng