Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja/ Kaduna

Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja/ Kaduna

- Hanyar Abuja zuwa Kaduna na cigaba da fuskantan barazanar yan bindiga

- A ranar Juma'a, kwamishanan tsaron Kaduna ya sanar musayar wuta tsakaninsu da Soji

- Ba'a samu daman kamasu amma an fitittikesu cikin daji

Rundunar Sojojin Operation Thunder Strike, OPTS, a daren Juma'a ta kawar da yunkurin da yan bindiga sukayi na garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnatin jihar Kaduna ta samu bayani daga jami'ai cewa yan bindiga sunyi kokarin kai hari a yankin Kasarami dake karamar hukumar Chikun misalin karfe 7:38 na dare.

Kwamishanan harkokin tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi cewa Sojoji na kan sintiri sukayi arangama da yan bindigan.

Jawabin yace yan bindigan sun gudu yayinda Sojoji suka kure musu gudu.

"Da dama cikin yan bindigan sun gudu da raunukan daga harsasai. Sojoji na binsu kuma za'a sanar da al'umma kan yadda ake ciki," yace

"Sauran Sojojin na kan hanyan domin bude hanyar da ta toshe sakamakon musayar bindigan."

"Gwamnatin jihar Kaduna na mai bada hakuri ga matafiya da suka fuskanci bacin lokaci sakamakon harin Sojojin. An yi hakan ne domin kare rayuka da dukiya," Aruwa ya kara.

KU DUBA: Black Friday: Fatawar Majalisar Malamai Kano ta shan banban da na Hisbah

Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja zuwa Kaduna
Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja zuwa Kaduna
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

A bangare guda, dattawan Arewa sun jinjinawa mai alfarma sarkin Musulumi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, kan abind asuka siffanta matsayin fadin gaskiya kan lamarin tsaro ya tabarbare a yankin.

A cewar dattawan, matsayar Sarkin Musulmi ne gaskiyar magana kan rashin tsaro a Arewa, kuma shine musababbin matsalar tsadar abinci da ake fama da shi a kasar gaba daya.

Dattawan karkashin gamayyar dattawan Arewa wajen neman zaben lafiya da cigaba, a jawabin da suka saki ranar Asabar, sun ce Sarkin Musulmi ya fiddasu kunya kan lamarin tsaro a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel