Black Friday: Fatawar Majalisar Malamai Kano ta shan banban da na Hisbah

Black Friday: Fatawar Majalisar Malamai Kano ta shan banban da na Hisbah

- Malamai a jihar Kano sun bayyana mabanbancin ra'ayi da hukumar Hisbah

- Hakazalika majalisar malaman Kano ta yi hannun riga da wasikan gargadin da Hisbah ta aike

- Ana bikin Black Friday ne a ranar Juma'a ta karshe na kowani watan Nuwamba a shekara

Fatawar majalisar malaman Kano ta sha ban-ban da na hukumar Hisbah kan lamarin ranar Black Friday da aka haramta fadinsa a jihar Kano don wasu dalilai.

Yayinda Hisbah take ganin Juma'a babbar rana ce kuma bai kamata a alakanta ta da wani abun aibi ba ko yaya ne, majalisar malamai na da ra'ayin babu laifi.

Shugaban majalisar malamai, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyanawa tashar rediyo, Freedom, cewa babu laifi cikin bikin ranar 'Black Friday'.

"Tun asali amfani da kalmar 'Black Friday' ba ya nufin mummunan abu, hasalima yabo ne," cewar Malam Khalil.

"Ba magana ce ta suka ba, in ka kalli tarihi, sai dai in mutum bai bincike abin da fadi ba."

Malamin ya kara da cewa bai san dalilin hukumar Hisbah na daukar matakin hana amfani da kalman da tayi ba, kuma idan da sunan addini ne to babu gabar kamawa.

KU DUBA: Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja/ Kaduna

Kan Black Friday, an samu sabani tsakanin Malaman Kano da Hisbah
Kan Black Friday, an samu sabani tsakanin Malaman Kano da Hisbah
Asali: UGC

A cewar wani malamin addini, Sheikh Abubakar Baban Gwale, yace babu laifi, bal ranan halastacce ne.

"Batun wanda suka kirkiri bikin ranar ko kiranta da 'Black Friday, ba za su sanya a haramta ta ba," yace

"Shi yasa yawancin fatawar malamai itace, babu laifi mutum yaci moriyar ranar ...amma kada ya sayi haramtattun kaya."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bukaci wata tashar radiyo da ta daina amfani da Kalmar ‘Black Friday’ wato "Baƙar Juma'a a jihar.

Black Friday kan kasancewa ranar Juma’a ta hudu a watan Nuwamba inda yan kasuwa ke zabtare farashin kayayyaki ga abokan cinikinsu gabannin bikin Kirsimeti.

A wata wasika mai kwanan wata 26 ga watan Nuwamba zuwa ga manajan tashar Cool FM a Kano, Abubakar Ali, wani jami’in Hisbah a madadin kwamanda Janar, ya ce mafi akasarin mazana jihar Musulmai ne wadanda ke kallon ranar a matsayin rana mai tsarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel