Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban

Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban

- Wata mata 'yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta yi ta yaudarar kanta tana tunanin maza za su kula da ita

- Maza 4 suka yaudareta duk ta haifa musu yara, amma suka juya mata baya suka barta da wahalar duniya

- Yanzu haka kwana take yi a shagon wani mutum tare da yaranta 4, cikin yunwa da kuncin rayuwa

Sophia Koji, wata mata 'yar kasar Ghana mai shekaru 31, ta bayyana yadda tayi ta yaudarar kanta, tayi tunanin maza za su iya kula da ita.

Kamar yadda matar ta bayyana a Crimecheckfoundation.org, tana da yara 4 wadanda ta haifa da maza daban-daban. Maimakon mazan su kula da ita da yaran, sai suka bar ta tana fama da wahalhalun rayuwa.

Sophia ta bayyana yadda ta koma kwana a shago, ita da yaranta sannan suka yi ta fama da yunwa da kishi saboda ta rasa kudaden shiga.

KU KARANTA: EFCC ta bayyana wani fitacce da suka hada kai da Maina wurin wawure kudin fansho

Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban
Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban. Hoto daga Crimecheckfoundation.org, Graphic.com.gh
Asali: UGC

A cewarta, "Akwai mutumin da nake tsarewa shago, duk ranar da ba mu yi ciniki ba za mu zauna da yunwa, ina bai wa wanda nake yi wa aiki kudaden.

"Ko da na gama siyar da kaya, sai ya ga dama zai biya ni. Akwai lokacin da ya bukaci yayi lalata dani, naki amincewa, tun daga nan ya fara cutar dani.

"Bayan na samu labarin Crime Check Foundation wadanda suke bai wa mata masu yara GHc 500 don su taimaka wa yaranta."

KU KARANTA: Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa

A wani labari na daban, jaruma Adesua Etomi ta caccaki hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie, a kan wasu hotunan da ta wallafa na nuna muhimmancin sanya takunkumin fuska, jaridar The Nation ta ruwaito.

Hotunan sun bayyana wasu yara sanye da takunkumin fuska wanda aka yi shi da kwali. Lauretta ta yi wa hotunan take da "Gwamnati ba ta umarci sanya takunkumin fuska ba don ta cutar da ku, ku kula da kawunanku. Ku dinga sakawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel