Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa

Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa

- Jam'iyyar APC ta jihar Legas ta fara fuskantar rabuwar kawuna tsakanin 'yan jam'iyya

- Wani jagoran jam'iyyar, Olajide Adeniran ya bayyana burinsa na zama gwamnan jihar a 2023

- A cewarsa, gwamnatin jihar ta yanzu, bata amfanar kowa sai mutane kalilan

Jam'iyyar APC ta jihar Legas ta fara fuskantar rabuwar kawuna cikin manyan 'yan jam'iyyar.

Olajide Adeniran, ya zargi gwamnatin jihar ta yanzu da damawa da mutane kalilan.

A wani taro da suka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, inda ya sanar da burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar da zarar Babajide Sanwo-Olu ya sauka, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

A cewarsa, zai yi nasara ya zama gwamna a 2023, duk da adawar jam'iyyar PDP. A cewarsa, mulkin Sanwo-Olu ya dade yana cutar dashi tun da kowa ya fahimci burinsa na zama gwamna.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata tare da dan na hannun daman Atiku Abubakar

Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa
Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa. Hoto daga @Asiwajutinubu
Source: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa Ganduje ya ke son kawo sauyi a tsarin masarautun Kano

A cewar Adeniran, yana so ya zama gwamna ne don ya dinga yi wa kowa aiki, ba wai ya kebe wasu daban su dinga amfana ba.

Kamar yadda yace: "Don ba mu durkusa wa kowa ba, ba mu yi laifi ba amma da izinin Ubangiji, ni zan zama gwamnan Legas a shekarar 2023.

"Ba zan bi wani shugaban jam'iyya ina rokonsa ba don ya mara min baya, ba na so in yi irin kuskuren da tsohon gwamnan jihar Legas yayi ba, Akinwunmi Ambode."

A wani labari na daban, Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya ta jam'iyyar APC, ya shawarci sanatocin da aka zaba ta jam'iyyar APC da su yi aiki tukuru na kokarin gyarawa APC sunanta a idon 'yan Najeriya.

Ya fadi hakan ne a wani taro da yayi da sanatocin APC a majalisar dattawa ranar Laraba, Buni ya ce wajibi ne jam'iyya mai mulki ta samu nasara a kowanne akwatin zabe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel