Kin tozarta kan ki a gida da ketare, Jaruma Adesua ta caccaki hadimar Buhari

Kin tozarta kan ki a gida da ketare, Jaruma Adesua ta caccaki hadimar Buhari

- Jarumar fina-finan Nollywood, Adesua Etomi ta caccaki Lauretta, wata hadimar Buhari

- Hadimar Buhari Lauretta ta wallafa hotunan wasu yara da takunkumin fuska na kwali

- A nan ne Adesua tace ta ji tausayin yaran, ire-iren Lauretta basa taimakon yaran da daga gani ba su da gata

Jaruma Adesua Etomi ta caccaki hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie, a kan wasu hotunan da ta wallafa na nuna muhimmancin sanya takunkumin fuska, jaridar The Nation ta ruwaito.

Hotunan sun bayyana wasu yara sanye da takunkumin fuska wanda aka yi shi da kwali. Lauretta ta yi wa hotunan take da "Gwamnati ba ta umarci sanya takunkumin fuska ba don ta cutar da ku, ku kula da kawunanku. Ku dinga sakawa.

"Wannan ce hanyar da za ku yi amfani da shi don kula da kawunanku, amma wasu suna ganin kamar takunkumi ba ya taimako wurin kariya. Ubangiji ya taimakemu."

KU KARANTA: Hotunan tubabbun barayin kayan tallafin korona suna rokon yafiya daga gwamnatin Filato

Kin tozarta kan ki a gida da ketare, Jaruma Adesua ta caccaki hadimar Buhari
Kin tozarta kan ki a gida da ketare, Jaruma Adesua ta caccaki hadimar Buhari. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Wannan wallafar bata yiwa Adesua Etomi dadi ba, inda tace hotunan sun bata mata rai har hakan ya sanya ta hawaye.

Adesua ta rubuta: "Kin tozarta kanki, a gida Najeriya da ketare. Ya kamata a ce kin ji kunyar wallafa yaran nan da kwalaye a fuskarsu, maimakon ku fara neman yadda za a yi a kawo karshen talauci don su samu su kare kawunansu daga cutar nan, amma kina nan kina kame-kame.

"Wannan hoton ya saka ni hawaye. Yaran kanana ne don haka ba za su iya kare kawunansu daga cutar ba. Kai!!! Wannan kasa.

"Na fara yarda da cewa wasu mutanen matattu ne amma a zahiri ne suke rayayyu."

KU KARANTA: Hisbah ta kama dan sandan da ke sace yaran mutane domin lalata da su a Kano

A wani labari na daban, wani mutum mai suna Olumuyiwa Johnson, mai yara 2, ya tabbatar wa da wata kotu da take Ibadan cewa ba zai iya zama da matarsa ba.

A cewarsa, aurensa mai shekaru 24 ya kare da matarsa saboda rashin kamun kanta da barazana ga rayuwarsa.

Olumuyiwa, wanda mazaunin wuraren Eleta ne a Ibadan, ya tabbatar wa da alkali Ademola Odunade, cewa matarsa tana barazana ga rayuwarsa bayan ya gano tana lalata da wasu kusoshin cocinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng