Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya

Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya

- A wasikar da lauyansu ya aikewa Kaakin majalisa, sun bukaci a biya diyya

- Tuni dai Gbajabiamila yayi alkawarin kula da iyalan mamacin kuma yaransa sun zama nasa

- Iyalan mamacin sun dauki Mike Ozekhome matsayin lauyansu

Iyalan Ifeanyi Okereke, mai sayar da jaridar da dogarin Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya kashe makon da ya gabata sun bukaci a biyasu diyyan milyan dari biya (N500m).

A wasikar da Lauyansu, Mike Ozekhome, ya aikewa Gbajabiamila, sun baiwa Kakakin kwanaki bakwai su biya kudin ko a kaishi kotu.

A wasika mai ranan wata 23 ga Nuwamba, Mr Ozekhome, ya ce mahaifin mamacin, Okorie Okereke, da kaninsa, Destiny Okereke, suka umurceshi ya bukaci kudin.

"Wadanda suka daukeni aiki sun bukaci wadannan abubuwa: Kayi amfani da ofis dinka mai alfarma wajen tabbatar da an hukunta hadiminka (Abdullahi Hassan) wanda ya kashe mutum bai gaira, ba dalili."

"Ka biya diyya ga iyalan Okereke da kudi N500,."

"Kudin ba zai dawo da rayuwar 'dansu, miji, da mai taimakonsu ba. Amma akalla zai taimaka musu wajen huce zafi."

"Ka sani cewa an bani umurnin idan baka biya wadannan bukatu ba ko kayi watsi da bukatun cikin kwanaki bakwai da rubuta wasikar nan, zamu shigar da kara kotu," wasikar yace.

KU KARANTA: Nan ba da dadewa ba zamu bude boda: Ministar Kudi, Zainab Shamsuna

Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya
Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya Hoto: Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: Fashola: Tsarin kama-kama ya na cikin ‘alkawarin’ jam’iyyar APC da ba a rubuta ba

Mun kawo muku rahoton cewa wani jami'in dan sanda dake gadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige wani mai sayar da jarida a birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis.

Kakakin majalisar da kansa ya tabbatar da hakan a shafinsa na Tuwita.

Kakakin majaisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana sunan dogarinsa da ya bindige wani mai sayar da jarida a Abuja, Ifeanyi Okereke, ranar Alhamis ba gaira ba dalili.

Gbjabiamila ya ce sunan jami'in tsaron Abdullahi Hassan, kuma tuni ya mika shi hannun hukumar DSS domin hukunta shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel