Yankin arewa ta tsakiya ne yake rike da makomar Najeriya, Bukola Saraki
- Najeriya gaba dayanta ta dogara ne da arewa ta tsakiya, cewar Dr Bukola Saraki
- Ya ce matsawar yankin ya bunkasa, Najeriya ta bunkasa, saboda tarin ma'adanan da ke yankin
- Saraki ya fadi hakan ne bayan shugabannin NCPF sun kai masa ziyara har gidansa da ke Abuja
A ranar Juma'a, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yankin arewa ta tsakiya za su ciyar da kasar nan gaba.
A cewar Saraki, yankin ne zai kawo mafita ga Najeriya nan gaba, The Nation ta ruwaito.
Kamar yadda yace, arewa ta tsakiyar tana da ma'adanai masu tarin yawa, wanda hakan zai kawo kudi Najeriya.
Saraki ya bayyana hakan ne bayan shugabannin kungiyar jama'an arewa ta tsakiya (NCPF) sun kai masa ziyara gidansa da ke Abuja.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata
A cewarsa, arewa ta tsakiya mallakin Najeriya ce, kuma wajibi ne a dubi yankin idan 2023 tayi.
KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba
An zabi tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin jigon NCPF, kuma ya nuna farincikinsa na wannan matsayi da aka bashi.
A cewarsa, babban dalilin kirkirar NCPF shine samar da hadin kan 'yan arewa gabadayansu, sannan da neman shawarwarin juna idan wani al'amari ya bullo.
A cewarsa, "Babban makasudin samar da kungiyar shine kawo cigaba. Yanzu haka hankalin al'umma kada ya koma kan siyasa. Gabadaya kasar nan sun dogara da arewa ta tsakiya saboda ma'adanan da yankin yake da su."
Saraki ya ce matsawar arewa ta tsakiya ta bunkasa, to Najeriya gaba dayanta ta bunkasa.
A wani labari na daban, wata jarumar fina-finan Nollywood 'yar asalin jihar Imo amma tashin jihar Kano, Juliet Njemanze, ta yi fina-finai masu kayatarwa kamar "Calabash", ta nuna da na saninta na zama jaruma.
Duk da jarumar ta karanta fannin shari'a a jami'a, sannan ta yi suna a harkar fina-finai, amma ta na jin takaicin kyamar da ake nuna mata a matsayinta na jaruma.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng