Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba

Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba

- Ban taba ciwo ba, balle in ziyarci asibiti, cewar wani tsoho mai shekaru 70

- A cewarsa, Ubangiji ne mai bayar da lafiya, don haka shi ya tsare shi

- Tsohon ya ce ya yi imani da Ubangiji, shiyasa cutuka basu samunsa

Wani tsoho mai shekaru 70 ya ce bai taba ciwo ba, tunda yake bai taba ziyartar asibiti ba don neman lafiya.

Tsohon mutumin dan kasar Ghana, ya ce ya yarda cewa Ubangiji ne mai bayar da lafiya.

A wata hira da gidan talabijin na SV Africa suka yi dashi, wanda Legit.ng ta kula da shi, mutumin ya ce Ubangiji yake bayar da lafiya.

Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba
Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba. Hoto daga svtvnetwork.com
Asali: UGC

Ya ce tunda yake a rayuwarsa, bai taba ciwo ba, ko kuma yaje asibiti ganin likita ba.

Mutumin ya kasance babban fasto kuma shugaban wata coci, wacce da kyar ka ji wani dan cocin ya fadi ciwo.

A cewarsa: "A matsayina na babban fasto, ba aikin ka bane ka yi ta sanar da mutane miyagun abubuwa da su ka samesu, babban aikinka shine ka taimakesu da kariya a kan cututtuka."

Da aka tambayesa dalinsa na rashin sanya takunkumin fuska, cewa tsohon yayi, ya kan sa, amma ba don kare kansa daga cutar coronavirus ba, don a tatsuniya ya dauketa. A cewarsa Ubangiji ne kadai zai iya karesa ba takunkumi ba.

KU KARANTA: Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida

KU KARANTA: Matasa sun yi caa kan budurwar da tace duk saurayin da bashi da N25m, kada yayi soyayya

A wani labari na daban, wata mata mai suna Katie Price, ta bayyana yadda take boye abinci don dakatar da jibgegen danta daga mugun ci.

A cewarta, har tsakar dare yake tashi yayi ta kwasar abinci yana ci, shiyasa yayi tulele, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Matar mai shekaru 42 ta bayyana yadda babban danta yake bubbula mata bangon dakuna idan ta hana shi cin abinci.

Harvey, mai shekaru 18 yana fama da wata cuta, wacce take sa shi yayi ta kwasar gara kamar Allah ya aiko shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng