Ina matukar jin kunyar bayyana cewa ni jarumar fina-finai ce, Juliet Njemanze

Ina matukar jin kunyar bayyana cewa ni jarumar fina-finai ce, Juliet Njemanze

- Ina matukar jin kunya idan aka kirani da jarumar fina-finai, cewar Jaruma Juliet Njemanze

- A cewarta, yadda ake yi musu kallon karuwai, kuma ake nuna musu tsana yana matukar tayar mata da hankali

- Jarumar ta fina-finan Nollywood ta bayyana hakan ne a wata tattaunawar ta da Potpourri

Wata jarumar fina-finan Nollywood 'yar asalin jihar Imo amma tashin jihar Kano, Juliet Njemanze, ta yi fina-finai masu kayatarwa kamar "Calabash", ta nuna da na saninta na zama jaruma.

Duk da jarumar ta karanta fannin shari'a a jami'a, sannan ta yi suna a harkar fina-finai, amma ta na jin takaicin kyamar da ake nuna mata a matsayinta na jaruma.

A wata tattaunawa da Potpourri suka yi da ita, kyakkyawar jarumar ta bayyana tsoronta, takaici da kuma burinta na nuna wa duniya yadda rayuwarta take, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci

A cewarta, "Ko wacce masana'anta tana da matsalolinta, amma abinda yafi bata min rai shine yadda mutane suke kyamata saboda sana'ata.

Ina matukar jin kunyar bayyana cewa ni jarumar fina-finai ce, Juliet Njemanze
Ina matukar jin kunyar bayyana cewa ni jarumar fina-finai ce, Juliet Njemanze. Hoto daga blueink.ng
Asali: UGC

"Yadda mutane suke nuna min kyama da tsana yana tayar min da hankali, wani lokacin har kunya nake ji idan aka kirani da jaruma, sai a dinga min kallon karuwa. Sun yarda da cewa duk sai darektoci da furodusoshi sun yi lalata da mace kafin ta kai inda take.

KU KARANTA: Innalillahi: Tsohon malami a KADPOLY ya harba matarsa tare da kashe kansa

"Ina matukar son sana'ar fim, amma gaskiya yadda mutane suke kallon mu ne yake daga min hankali.

"Sannan yadda ake biyanmu yana bata min rai, saboda in dai mutum ba tauraro bane, ba ya samun kudi sosai. Kuma da farko na sha wahala a ma'aikatar nan, saboda ba a wani biyana, amma daga baya na samu na wuce wurin."

"Akwai darektoci da furodusoshi da za su yi ta maka alkawarin karya duk don su mori jikin mace, amma da zarar sun samu shikenan," tace.

A wani labari na daban, kungiyar 'yan sanda masu taimakon gaggawa (RRS) na jihar Legas ta sanar da yadda jami'anta suka samu nasarar ceto jakar wata mata mai cike da makudan kudade, kuma suka maida mata.

A cewarsu, jami'an RRS suna cikin sintiri wuraren Igando, sai suka hangi jakar wata mata ta fado daga babur. Sun dauka har suka nemi sanar da dan acaban da yake tuka ta amma abin ya ci tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng