'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata
- 'Yan sanda masu taimakon gaggawa sun bi wata mata har gida, inda suka mayar mata da jakarta
- Jakar matar mai cike da makudan kudade da wayarta ta fadi daga kan babur ba tare da ta sani ba
- 'Yan sandan sun nemi sanar da dan acaban da ke tuka ta amma abin ya ci tura
Kungiyar 'yan sanda masu taimakon gaggawa (RRS) na jihar Legas ta sanar da yadda jami'anta suka samu nasarar ceto jakar wata mata mai cike da makudan kudade, kuma suka maida mata.
A cewarsu, jami'an RRS suna cikin sintiri wuraren Igando, sai suka hangi jakar wata mata ta fado daga babur. Sun dauka har suka nemi sanar da dan acaban da yake tuka ta amma abin ya ci tura.
Take a nan suka bi bayansu, har sai da suka tabbatar sun mayar wa da matar jakarta.
Sun wallafa hotunan wasu jami'an suna mika wa wata mata jaka, inda su ka wallafa a shafinsu na Twitter:
KU KARANTA: FG ta saki N5.2bn domin ginin gidajen 'yan gudun hijira, Zulum
"Jami'an RRS suna cikin sintiri da yammacin nan wuraren Igando, sai suka hangi wata jar jaka ta fado daga babur. Sun dauki jakar, har su ka nemi sanar da dan acaban, amma ya yi tunanin tsare shi za su yi sai ya gudu.
"A hankali su ka bi bayansa, har inda matar za ta sauka, suka mika mata jakarta. Sai da ta kirga kudinta na cikin jakar N115,000 da wata waya kirar Tecno a cikin jakar. Babu abinda ya bata."
KU KARANTA: Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci
A wani labari na daban, ana zargin wani mutum dan Atlanta da yi wa budurwarsa da suka hadu a wata kafar sada zumunta dukan tsiya, bayan sun hadu ido da ido, shafin Linda ikeji.
Ana zargin ya daki budurwar ne, saboda ta zabi abubuwa masu tsada, shiyasa ya daki kudinsa. Benjamin Francher ya shirya haduwa da Brittany Correri a daren Laraba, 11 ga watan Nuwamba. A ranar haduwarsu ta farko, ya mutunta 'yan uwanta da iyayenta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng