ASUU: Kada dalibai da iyaye su yi tsammanin za mu koma nan kusa

ASUU: Kada dalibai da iyaye su yi tsammanin za mu koma nan kusa

- Kada ku sa ran komawarmu makarantu, nan kusa, cewar ASUU ga dalibai da iyayensu, sannan malamai su nemi wata halastacciyar hanyar samun kudi

- Shugaban kungiyar, na yankin Abuja, ya sanar da hakan a wani taro da suka yi a Abuja, inda yace gwamnati ta yi wa ASUU rikon sakainar kashi

- Sannan babban abin mamaki shine yadda ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya fito yace an biya malamai albashi, duk da ya san ba hakan bane

Jiya ASUU ta ce kada iyaye ko dalibai su sa ran za su dakatar da yajin aikinsu nan kusa, inda ta shawarci malaman jami'a da su yi kokarin samun wata hanyar samun na tuwo.

Shugaban kungiyar na yankin Abuja, Farfesa Theophilus Lagi, ya sanar da hakan a wani taro da suka yi a jami'ar Abuja, inda yace za a cigaba da zaman gida har sai gwamnati ta yi abinda suke so.

Ta zargi gwamnatin tarayya da nuna halin ko in kula ga harkar ilimi.

Kamar yadda shugaban kungiyar yace: "Yau ina so in sanar da 'yan Najeriya, musamman dalibai da iyaye cewa, kada su sa ran ASUU za ta dakatar da yajin aikinta wanda ta fara tsawon watanni da suka gabata, saboda har yanzu gwamnati bata nuna damuwarta ba wurin samar da abubuwan da suka kamata.

"Muna shawartar 'yan kungiyarmu da su nemi wata hanyar samun kudi na halas, saboda gwamnati ta rike mana albashi tun na watan Fabrairun 2020."

Kungiyar ta zargi ministan kwadago da ayyuka, Dr Chris Ngige da yin talalabiya ga harkokin ilimin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Kungiyar ta ce Ngige ya fara shisshigi da zakewa, don har ya zama kakakin babban akawun tarayya, maimakon nemo mafita ga malamai. Ya mayar da hannun agogo baya. Ya nuna kiyayya karara ga ASUU.

"Har mamaki Ngige ya bamu, yadda ya fito gaban kowa babu kunya ba tsoron Allah, yana sanar da duniya cewa an biya malamai kudadensu, wadannan kalaman sun rage darajarsa, duk da ya san ba a biya albashin ba, tun na watanni 6 zuwa 9 da suka gabata." yace.

KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

ASUU: Kada dalibai da iyaye su yi tsammanin za mu koma nan kusa
ASUU: Kada dalibai da iyaye su yi tsammanin za mu koma nan kusa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan dan Najeriya da ya garzaya kasar waje ya yi wuff da zukekiyar budurwa sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya ce tashin farashin man fetur ya auku ne saboda wani kamfanin hada magunguna na Amurika, Pfizer ya bayyana riga-kafin cutar COVID-19.

Sylva ya fadi hakan ne a wata ganawar sirri da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Lahadi, inda ya sanar da manema labarai cewa samun riga kafin cutar COVID-19 shine sanadiyyar tashin kudin man fetur a kasuwannin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel