FG ta bayyana dalilin tashin farashin man fetur zuwa N170

FG ta bayyana dalilin tashin farashin man fetur zuwa N170

- Karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya fadi dalilin tashin farashin mai

- A cewarsa, tun bayan da Pfizer suka bayyana riga-kafin cutar COVID- 19 komai ya tashi

- Ya kara da cewa, matsawar farashin mai ya tashi, farashin komai yana tashi

Karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya ce tashin farashin man fetur ya auku ne saboda wani kamfanin hada magunguna na Amurika, Pfizer ya bayyana riga-kafin cutar COVID-19.

Sylva ya fadi hakan ne a wata ganawar sirri da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Lahadi, inda ya sanar da manema labarai cewa samun riga kafin cutar COVID-19 shine sanadiyyar tashin kudin man fetur a kasuwannin duniya.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7

"Tashin farashin man fetur ya auku ne sakamakon sanar da riga-kafin cutar COVID-19 da Pfizer sukayi. Idan an lura, farashin ya karu ne bayan sanar da samuwar riga-kafin.

"Matsawar kudin mai ya tashi, yana nufin farshin sauran kayan masarufi ya karu, haka kuma duk wani abu da aka tace, kudinsa zai karu," a cewarsa.

FG ta bayyana dalilin tashin farashin man fetur zuwa N170
FG ta bayyana dalilin tashin farashin man fetur zuwa N170. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda jami'an SARS ci zarafina tare da watsa min barkonon tsohuwa, Gwamnan APC

A wani labari na daban, Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, Johnson Kokumo, ya ce 'yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannu 'yan ta'adda su na kashesu kamar kaji ba.

A ranar Litinin, Kokumo ya fadi hakan a wani taro na kaddamar da kungiyar 'yan sa kai 70 a karamar hukumar Ikopaba-Okha da ke jihar.

Ya bayyana asalin manufar zanga-zangar EndSARS, inda yace dan sa ya kashe kansa bayan masu zanga-zangar sun janyo masa asarar naira miliyan 7.

A cewarsa, kamata yayi a ce 'yan sanda sun yi amfani da makamai wurin kare rayuwarsu da ta wasu mutane, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel