'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

- Ba za ta sabu ba, kare ya kashe ragon layya, cewar kwamishinan 'yan sanda na jihar Edo

- A cewarsa, babu dan sandan da zai sake bari dan ta'adda ya cutar da shi

- Ya ce ba zai bar dan ta'adda mai rike da wuka, ya kashe dan sanda mai AK-47 ba

Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, Johnson Kokumo, ya ce 'yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannu 'yan ta'adda su na kashesu kamar kaji ba.

A ranar Litinin, Kokumo ya fadi hakan a wani taro na kaddamar da kungiyar 'yan sa kai 70 a karamar hukumar Ikopaba-Okha da ke jihar.

Ya bayyana asalin manufar zanga-zangar EndSARS, inda yace dan sa ya kashe kansa bayan masu zanga-zangar sun janyo masa asarar naira miliyan 7.

A cewarsa, kamata yayi a ce 'yan sanda sun yi amfani da makamai wurin kare rayuwarsu da ta wasu mutane, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ya ce za su cigaba da fadi wa 'yan sanda cewa kada su yi zalunci, amma kada su kuskura su bari wani dan ta'adda mai wuka ya kashe dan sanda mai AK-47.

Ya kara da cewa, "Yan sanda ba za su tsaya su mutu a hannun 'yan ta'adda ba. Kuma ina so kowa ya sanar da makwabtansa da yaransa wannan sakon."

KU KARANTA: Yadda jami'an SARS ci zarafina tare da watsa min barkonon tsohuwa, Gwamnan APC

'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina
'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

A wani labari na daban, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce PDP ce babban abokin Najeriya. Atiku ya ce PDP ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 kafin APC ta amshi mulkin Najeriya a 2015.

Atiku ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, inda yace, "PDP ce babban abokin Najeriya. Duk bangarorin Najeriya suna bukatar jam'iyyar da za ta gyara Najeriya, ba wacce za ta lalata ta ba.

"Jam'iyyar PDP ta tabbatar da za ta gyara Najeriya, sannan ina rokon 'yan Najeriya da su amince da jam'iyyar don za ta tabbatar da adalci ga kowa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng