Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana halacci ba - Ohanaeze Ndigbo

Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana halacci ba - Ohanaeze Ndigbo

- Kungiyar Ohaneze Ndigbo ta nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar Ebonyi

- Dave Umahi ya bayyana niyyarsa na son sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress APC

- Babban jigon Ohaneze ya ce PDP za tayi butulci idan bata baiwa Igbo shugabancin kasa ba

Kungiyar yan kabilar Igbo a gida da waje, Ohanaeze Ndigbo, ta amince da kokarin sauya shekar da gwamnan Ebonyi, David Umahi, keyi daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress APC.

An ruwaito cewa Umahi ya bayyanawa jagororin uwar jam'iyyar PDP a wata ganawa a Abuja, ranar Talata, cewa yana son fita daga jam'iyyar ne saboda an ki baiwa yankin Igbo kujerar shugabancin kasa a 2023.

Mataimakin Kakakin Ohanaeze, Cif Chuks Ibegbu, ya siffanta sauya shekar Umahi matsayin aikin kwarai.

Ibegbu ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch a Enugu ranar Laraba.

Ya ce PDP za ta yi rashin hallaci idan bata baiwa yankin Igbo kujerar takarar shugaban kasa a 2023 ba.

KU KARANTA: Bayan lallasa APC a zabe, ana bikin rantsar da Godwin Obaseki wa'adi na 2 (Hotuna)

Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana hallaci ba - Ohanaeze Ndigbo
Mun amince da komawar Gwamna Ebonyi APC, PDP ba tayi mana hallaci ba - Ohanaeze Ndigbo Hoto: Presidency
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan tashin Bam na jiya a Saudiyya, an kai hari ofishin jakadancin kasar dake Hague

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya gaya wa shugabancin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata cewa zai bar jam'iyyar.

Ya ce zai koma jam'iyya mai mulki ta APC yana mai ikirarin cewa APCn zata bawa dan yankin sa na kudu maso gabas takara a zaben 2023.

Umahi ya kuma bayyana cewa ya riga ya yanke shawara kuma bazai chanja ba.

Shugabannin da suka jagoranci taron sun yi kokarin gamsar da gwamnan kada ya bar jam'iyyar amma a banza.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel